Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo Da Naira Biliyan 50, Gwamnatin Tinubu

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo Da Naira Biliyan 50, Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnatin tarayya ta yi martani a kan batun yin sasanci da Godwin Emefiele da ake kotu da shi
  • Ministan shari’a ya karyata jita-jitar cewa za a karbi kudi daga hannun tsohon gwamnan CBN
  • Sanarwar da aka samu daga AGF ta yi watsi da labarin duk da maganar da lauyoyi su ka yi a baya

Abuja - Gwamnatin tarayya ta karyata jita-jita da ke nuna kulla yarjejeniya da tsohon gwamnan babban banki na CBN, Godwin Emefiele.

A wani jawabi da aka fitar daga ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya, The Nation ta ce gwamnatin Najeriya ta musanya jita-jitar.

Kamar yadda AGF ya sanar a ranar Lahadi, 1 ga Oktoba 2023, babu inda aka cin ma matsaya duk da lauyoyin Emefiele sun kawo maganar.

Bankin CBN
Ana binciken tsohon Gwamnan CBN Hoto: @Cenbank
Asali: Twitter

"Babu sulhu da Godwin Emefiele"

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

Da ake shari’a a kotu, masu kare korarren gwamnan babban bankin kasar sun bijiro da batun sulhu, har yanzu ba a kammla shari'ar ba tukun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin da aka fitar a karshen makon jiya ya samu sa hannun Darektan labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar shari’a ta kasa, Modupe Ogundoro.

Mista Modupe Ogundoro yake cewa babu inda aka yi wannan yarjejeniya, har a ce abin da ya rage shi ne sa hannun mai girma shugaba Bola Tinubu.

Idan rahoton da aka fitar gaskiya ne, gwamnatin tarayya za ta karbi wasu makudan kudi daga hannun Emefiele, sai a daina shari’a da shi a kotu.

Jawabin AGF a kan shari'ar Godwin Emefiele

Sai dai, babu inda aka cin ma wannan yarjejeniya da Mr Godwin Emefiele ko kuwa wakilansa.
Ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya na mai tabbatarwa karara cewa wadannan rahotanni tsan-tsa-gwaron karya ne.

Kara karanta wannan

Yajin-Aiki: Tinubu Ya Karawa Ma’aikata N10, 000 a Yunkurin Lallabar ‘Yan Kwadago

Mu na so mu yi kira ga ‘yan jarida da sauran al’umma su yi watsi da rahoton nan na bogi.
Ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a zai cigaba da yin duk abubuwan da su ka dace da kishin al’umma.

- Modupe Ogundoro

CBN sun yi sabon Gwamna

Kwanakin baya aka ji Majalisar dattawan Najeriya ta tantance Mista Yemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban banki na kasa (CBN).

Yemi Cardoso ya maye gurbin Godwin Emefiele duk da dakatar da shi aka yi, a maimakon tsige shi daga aiki kamar yadda doka ta tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel