Direba Ya Cakawa Jami'in LASTMA Wuka a Legas, Ya Yi Tumbur Daga Baya

Direba Ya Cakawa Jami'in LASTMA Wuka a Legas, Ya Yi Tumbur Daga Baya

  • Rundunar ƴan sanda ta cafke wani direban motar bas da laifin cakawa jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) wuƙa
  • An tattaro cewa lamarin ya auku ne a kusa da shataletalen Costain da ke jihar Legas a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba
  • A wata sanarwa da hukumar LASTMA ta fitar, ta zargi direban da laifin karya dokar hanya kuma ya ƙi yarda a cafke shi bayan aikata laifin

Jihar Legas - Wani abin al'ajabi ya auku a kusa da shataletalen Costain a jihar Legas a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba, a tsakanin direban motar danfo da wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA).

A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar ta ce jami’an hukumar LASTMA sun dakatar da direban danfon ne bisa zarginsa da karya dokar tuƙi.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Malaman jami'a sun ci taliyar karshe saboda aikata badala da rashawa

Direba ya cakawa jami'in LASTMA wuka a Legas
Direban motar bas ya yi tsirara bayan ya cakawa jami'in LASTAMA wuka a Legas Hoto: @followlastma
Asali: Twitter

Rahoton ya tabbatar da cewa direban da har yanzu ba a tantance ko waye ba, ya illata ɗaya daga cikin jami’an LASTMA da wuƙa a wurin da lamarin ya auku, cewar ahoton Vanguard.

Meyasa direban ya yi tsirara?

A wurin da lamarin ya auku, an tattaro cewa direban mai mota mai lamba LSR 966 YE, an nuna shi a wani faifan bidiyo yana yin tsirara domin nuna tirjiya ga jami’an LASTMA da suka tare shi bisa laifin karya dokar tuƙi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ji shi a cikin faifan bidiyon yana cewa, "Ba za ku iya ɗaukar wannan motar daga nan ba" kamar yadda aka gan shi a cikin bidiyon yana yin magana da wani ta wayar salula.

An kuma jiyo wata murya tana gaya wa jami'an LASTMA da ke cikin motar ɗin cewa, "Wannan mutumin dole sai an kai shi gidan gyaran hali."

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da gobara ta lamushe fitaccen kamfanin robobi a jihar kasuwanci

A wani faifan bidiyo, an ga direban wanda ya tube tsirara yana tsaye akan motar jami’an LASTMA wacce aka rubuta 'Zone 3, Surulere' a jikinta.

LASTMA ta fitar da sanarwa a hukumance

Da take bayar da karin bayani kan lamarin a shafinta na X mai suna @followlastma, hukumar ta tabbatar da cewa ƴan sanda sun yi caraf da direban

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A ranar Lahadi 24/09/2023 jami'an LASTMA sun kama wata motar bas ƙirar T4 (LSR 966 YE) saboda haifar da cikas ga sauran masu amfani da hanyar a kusa da Costain."
"Direban motar bas ɗin ta T4 da aka kama ya haifar da hayaniya inda ya tube kansa tsirara a bainar jama'a bayan ya cakawa jami'in LASTMA wuka."

An tattaro cewa daga karshe jami’an ƴan sanda daga ofishin ƴan sanda na Iponri sun cafke direban da ya yi tsirara bisa umarnin DPO na yankin.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Magidanci Ya Bayyana Yadda Rusau Din Gwamnati Ya Jawo Matarsa Mai Juna Biyu Ta Rasu

Direba Ya Murkushe Kan Jami'in FRSC

A wani labarin kuma, wani direban babbar mota ya murƙushe jami'in hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar Legas.

Jami'in ya ce ga garinku nan bayan direban babbar motar ya matse shi a jikin wata mota lokacin da yake ƙoƙarin kaucewa kamu daga wajen jami'an hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel