Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m

Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m

- Wani direba da ya dauko karuwa ta tsere da motar maigidansa na N5.4m

- An gurfanar da direban gaban kotu kan hadin baki da sata

- Sai dai direban ya musanta zargin da ake masa inda ya ce shima bai dade na haduwa da budurwar ba

Wani direban kamfanin samarwa mutane aiki da ke Awolowo Road da ke Ikoyi a Legas ya jefa kansa a rigima bayan wata budurwa da ya dauka a titi ta tsere da motar mai gidansa kirar Kia Sorento wanda kudinta ya kai N5.4m.

Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m
Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m
Asali: Twitter

Budurwar mai suna Nina ta tsere da motan ne a gidan mai yayin da direban motan, Victor Dossa ya sauka daga motar domin ya duba yadda ake zuba masa mai a motar.

DUBA WANNAN: Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an shigar da kara ofishin 'yan sanda da ke Onikan kuma an kama direban wanda asalinsa dan Jamhuriyar Benin ne.

Daga bisani an gurfanar da Dossa a kotun Majistare da ke Igbosere inda dan sanda mai shigar da kara, Saja Francisca Job ya karanto cewa ana tuhumar Dossa da aikata laifiin hadin baki da sata.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Y.O. Aro-Lambo ya bayar da belinsa a kan kudi N1 miliyan da mutane biyu da za su tsaya masa.

An daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Satumban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164