Magidanci Ya Bayyana Yadda Matarsa Mai Juna Biyu Ta Rasu Bayan Gwamnati Ta Rusa Gidansu a Legas

Magidanci Ya Bayyana Yadda Matarsa Mai Juna Biyu Ta Rasu Bayan Gwamnati Ta Rusa Gidansu a Legas

  • An zargi gwamnatin jihar Legas a ƙarƙashin gwamna Babajide Sanwo-Olu da rusa wani gida ba tare da bayar da sanarwa ba
  • A watan Yuli ne aka rushe gidan Mista Joshua Vandi a yankin Oworonshoki na jihar duk da roƙon da matarsa ​​mai ciki da ƴaƴansa uku suka yi
  • Mista Vendi, a wata hira da aka yi da shi, ya ce matarsa ​​ta rasu ne sakamakon tashin hankalin da ta shiga saboda ruguza musu gida

Oworonshoki, Legas - Wani magidanci mai shekara 36 a duniya ɗan asalin ƙaramar hukumar Michika ta jihar Adamawa, Mista Joshua Vendi, ya bayyana yadda matarsa ​​mai juna biyu ta rasu sakamakon tashin hankalin da ta shiga bayan gwamnatin jihar Legas ta ruguza musu gida.

A wata hira da jaridar The Punch, Mista Vendi, wanda gidansa ke a unguwar Oworonshoki a jihar Legas, ya ce aikin rusau ɗin ya faru ne a watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

Magidanci ya rasa gidansa bayan gwamnati ta rusa masa gidansa
Mista Vendi ya ce ya rasa gidansa ne bayan gwamnatin Legas ta rusa masa gida Hoto: Babajide Sanwo-Olu/Lasbca
Asali: Facebook

Vendi, mai kula da gidaje a wani asibitin kwararru da ke jihar Legas, ya ce matarsa ​​Ladi "ta rasu ne a asibitin Afolabi Memorial Hospital, da ke titin Oworo."

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Abin da ya faru shi ne, a matsayina na mazaunin Oworonshoki, da ke kan titin Odunfa 33, ina da fili na. Na sayi fili ɗaya da rabi daga wajen asalin masu shi, inda na gina gida wanda ni da matata muka zauna a ciki kusan shekara biyu."
"A wannan ranar, ina wurin aiki lokacin da tawagar jami'an da suka ruguza gidan suka zo."

Mista Vendi ya ce babu wata sanarwa da gwamnatin Legas ta bayar

Da aka tambaye shi ko ya samu sanarwar tashi kafin a rusa ginin, Mista Vendi ya ce babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Legas.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Legas ma ba ta biya shi diyya ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Ɗau Zafi, Ya Tona Asirin Alakar Wasu 'Yan Siyasa da Kashe-Kashen Mutane a Jihar Arewa

Vendi ya bayyana cewa a lokacin da ya isa gidan, ya roki mai kula da aikin rushewar da ya duba halin da matarsa ​​ke ciki.

Da aka tambaye shi ko wacce irin amsa ya ba shi, Vendi sai ya kada baki yace:

"Ya ce min idan ina da koke, na je sakatariyarsu da ke Alausa, Legas, ya dage sai ya ruguza min gidana, ya ce gara na shiga na kwashe duk wani abu mai muhimmanci."

Mista Vendi ya bayyana cewa matarsa ​​ba ta sake farfaɗowa ba daga kaɗuwar abin da ta gani a wurin da lamarin ya faru ba kafin ta rasu.

Ya bayyana cewa yana da ƴaƴa uku masu shekara takwas, huɗu da biyu.

Wike Ya Ruguza Kasuwa a FCT

A wani labarin kuma, ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, na cigaba da ganin ya dawo da birnin bisa kan ainihin tsarinsa na farko.

Hukumar FCTA masu kula da birnin tarayya Abuja sun ruguza wata kasuwa da mutane su ka sani da ‘Kasuwar Dare’.

Asali: Legit.ng

Online view pixel