Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in FRSC a Jihar Legas

Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in FRSC a Jihar Legas

  • Wani jami'in hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) ya riga mu gidan gaskiya a wani hatsarin da ya auku a jihar Legas
  • Jami'in mai suna Abiodun Ajomole, ya mutu ne a lokacin da wata babbar mota da bata da birki ta haɗe shi da wata motar bas da yake bincike
  • Rundunar ƴan sanda ta fara bincike domin gano inda direban babbar motar yake wanda ya jawo aukuwar hatsari

Ikeja, jihar Legas - Wani jami’in hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) ya mutu har lahira a unguwar Orile-Iganmu a jihar Legas.

Jaridar TheCable ta ce shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami'in, an matse shi ne a jikin wasu manyan motoci guda biyu har sai da ya mutu.

Jami'in FRSC ya rasa ransa
Direban babbar mota ya halaka jami'in FRSC a Legas Hoto: Federal Road Safety Corps Nigeria, the Cable
Asali: Facebook

Bisi Kazeem, kakakin hukumar FRSC, ya tabbatarwa da jaridar The Cable wannan mummunan hatsarin. Ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Wasu Motoci Sun Yi Taho Mu Gama

Rahotanni sun ce direban babbar motar da ya yi karo da jami’in hukumar FRSC ɗin, yana kokarin kaucewa binciken jami'an hukumar ne a lokacin da lamarin ya auku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki hukumomin tsaro ke ɗauka?

Kazeem bai bayyana ko an cafke direban babbar motar a sakamakon aukuwar hatsarin ba, amma gidan talabijin na TVC ya rahoto cewa jami'an ƴan sanda na Orile da aka sanar da aukuwar lamarin, ta aike da jami’anta yayin da jami’an LASTMA suma suka garzaya wurin domin ceto.

Jaridar The New Telegraph ta ƙara da cewa, tuni ƴan sanda suka bazama aiki domin gano inda direban babbar motar ƙirar Mack Truck yake, wanda yake da alhakin aukuwar hatsarin a yayin da ake cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Rayukan Mutum 5 Sun Salwanta a Wani Hatsari

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa rayukan mutane biyar sun salwanta a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da wasu motoci akan titin Legas zuwa Ibadan.

Hatsarin motan wanda ya auku a kusa sansanin Foursquare da ke akan titin, ya ritsa da motoci masu yawa bayan tayar wata babbar mota ta yi bindiga saboda tsananin gudun da take yi akan titin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel