Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah

Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah

- Wani direban mota ya basga wa jami'in LASTMA tabarya a kai a ranar Talata, 8 ga watan Disamba

- Hakan ya faru saboda jami'in ya dakatar da direban a kan karya dokar tuki wuraren Jakande a Lekki

- Tuni aka garzaya da direban ofishin 'yan sanda da ke Ilasan don daukar hukunci da bincike

An kama wani direban mota, Fred Onwuche, saboda amfani da tabarya wurin ji wa wani jami'in LASTMA ciwo a Kosoko Rasak, wuraran Jakande a Lekki jihar Legas.

Al'amarin ya faru ne a ranar Talata, 8 ga watan Disamba kamar yadda wata takarda daga ofishin shugaban LASTMA, Olajide Oduyoye ta sanar. Ta tabbatar da yadda jami'in ya tsayar da direban saboda karya doka yayin tuki.

Hakan ya fusata Onwenche, inda yayi gaggawar dakko tabarya ya buga wa kan jami'in LASTMA a kai, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah
Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)

Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah
Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

"An yi gaggawar tafiya da Rasaq asibiti don samun taimako na gaggawa sakamakon yadda jini yayi ta zuba saboda yankan. Sannan an tafi da Onwuche ofishin 'yan sanda da ke Ilasan don yanke masa hukunci da cigaba da bincike.

"Wajibi ne ya fuskanci fushin hukuma. Hukuma ba za ta saurara masa ba, don ya sanya abokai, 'yan uwa da iyalan Razak cikin takaici da bakin ciki," kamar yadda manajan yace.

"Wannan ba shine karo na farko da ake kai wa jami'an LASTMA farmaki ba. Wasu daga cikinsu har kashesu suna kan aiki ake yi" cewar Oduoye.

Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah
Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa

Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah
Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

A wani labari na daban, mazauna kananun hukumomin Gudu da Tangaza da ke jihar Sokoto, sun koka a kan yadda al'amuran 'yan bindiga suka takura su har suke kai ga neman wurin rabewa a kasar Nijar.

A cewarsu, 'yan bindiga suna zuwa garuruwansu da yamma, su amshe dukiyoyi masu tarin yawa daga hannayen masu hali a cikinsu, ko kuma su yi garkuwa da su.

Daya daga cikin mazauna kauyen Kurdula, ya bayyana wa BBC cewa da yawansu suna tserewa kasar Nijar da yamma sai su koma gidajensu da safe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel