Wike Ya Cigaba da Rusau a Abuja, Hukuma Ta Rugurgaza Kasuwar Dare a Asokoro

Wike Ya Cigaba da Rusau a Abuja, Hukuma Ta Rugurgaza Kasuwar Dare a Asokoro

  • A makon nan aka ruguza Kasuwar Dare a wani karon, ana zargin wurin ya zama mafakar miyagu
  • Hukumar FCTA ta tabbatar da cewa ‘yan kwaya da tsageru su na yin ta’adi a wurin neman abincin
  • Wannan ya na cikin yunkurin da ake yi na dawo da martabar Abuja bayan an yi canjin gwamnati

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Jami’an hukumar FCTA masu kula da birnin tarayya Abuja sun ruguza wata kasuwa da mutane su ka sani da ‘Kasuwar Dare’ a makon nan.

Premium Times ta ce ana zargin kasuwar da ke kan titin Hassan Musa Katsina a kusa da Kpaduma II a Asokoro Ext. ta zama wata mafarkar miyagu.

Dillalan kwayoyi da marasa gaskiya su na cikin wadanda ake zargin su na fakewa da kasuwar, Nyesom Wike yayi alkawarin maganin marasa gaskiya.

Kara karanta wannan

Sabon Minista Nyesom Wike Ya Fara Aiki, An Rugurguza Katafaren Gini a Abuja Har Kasa

Kasuwar Dare a Asokoro
Kasuwar dare da aka rusa a Abuja Hoto: nannews.ng
Asali: UGC

Abuja: Meyasa aka rusa kasuwar dare?

A wata zantawa da NAN ta yi da Darektan kula da cigaba na hukumar FCTA, Mukhtar Galadima, ya zayyana hikimar rugurguza wurin sana’ar jama’an.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Mukhtar Galadima ya ce kasuwar ta zama masifa ga mazauna yankin da masu bin hanyar saboda ta zama matattara mugayen iri a birnin Abuja.

Rusa kasuwar da aka yi ya na cikin kokarin FCTA na ganin ta tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya, ‘yan kwanaki bayan an nada ministoci.

An taba ruguza kasuwar sau 3

Daily Trust ta ce ba wannan ne karon farko da kasuwar ta je kasa ba, an yi irin haka a baya amma aka cigaba da sake tada gini domin a iya cigaba da harkoki.

Babban jami’in yake cewa ta kai miyagu su na ta’adi kuru-kuru, saboda haka ya zama dole hukuma ta dauki, Galadima ya ce ba za su bari a cigaba da haka ba.

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

"Wannan aiki da aka yi zai taimaka mana wajen ganin bayan tsageru da dillalan kwaya da su ka karbe wurin.
Mun ruguza wurin kusan sau uku, amma wadannan bata-gari su ka sake ginawa, su ka cigaba da aika-aikarsu.
Wannan karo kasuwar za ta cigaba da zama a ruguje. Mu na bukatar tsabtace wurin, a inganta kyawun wurin."

- Mukhtar Galadima

Mutanen Abuja sun shiga dar-dar

Tun da Nyesom Wike ya zama ministan birnin tarayya, ya sha alwashin dawo da martabar Abuja, a ranar farko ya shaida cewa za a ruguza gine-gine.

Rahoto ya zo cewa babu mamaki rusau zai iya shafar mazauna Dei Dei, Durumi, Dutse, Garki, Nyanya, Piya Kasa, Gishiri da Apo a babban Birnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel