Rusau: Abba Kabir Ya Ce Ba Za Su Yi Asara Ba, Zai Yi Amfani Da Burbushin Rushe-rushen Don Gyara Ganuwoyin Kano

Rusau: Abba Kabir Ya Ce Ba Za Su Yi Asara Ba, Zai Yi Amfani Da Burbushin Rushe-rushen Don Gyara Ganuwoyin Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta yi amfani da burbushin rushe-rushen da aka gudanar don sake gina da kuma gyara ganuwoyin birnin Kano
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ziyarar gani da ido a wuraren da aka gudanar da rushe-rushen don ganin yadda aikin ke tafiya
  • Ya roki mutane a jihar da su zama masu bin dokar kasa da kuma kai rahoton duk wani abu da basu yarda da shi ba ga jami'an tsaro

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta yi amfani da burbushin rushe-rushen da aka yi don gyara katangun jihar.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf shi ya bayyana haka yayin ziyarar gani da ido da ya kai wurare da dama da aka rushe a birnin Kano.

Abba Gida Gida ya ce zai yi amfani da burbushin rushe-rushe don gyara ganuwoyin Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

A ranar Juma'a 16 ga watan Yuni, kwamitin da gwamnan ya kafa ya ci gaba da rushe wasu wurare da ake tunanin an gina su ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Abba Kabir ya umarci a tsare wuraren da aka rusan don masu sata

Daga cikin wuraren akwai shataletalen da ke kusa da Gidan Gwamnati da gidan sama mai dauke da shaguna 90 a karamar hukumar Nasarawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran sun hada da shaguna da dama da ke kusa da shingen filin wasa na Sani Abacha a kofar mata da sauransu, cewar TheCable.

Gwamnan ya ce ya umarci jami'an tsaro da kuma hukumar tsaro ta NSCDC da su kula da wuraren da aka rushen don hana mutane sata.

A cewarsa:

"Mun zagaya duk inda aka yi rusau kuma mun yanke shawarar zamu yi amfani da burbushin don gyara ganuwoyin birnin Kano domin ci gaba da dabbaka tarihi.
"Hakan zai kawata birnin Kano, da kuma inganta ganuwar ya yi kyau don inganta harkar masu yawon bude ido."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

Gwamnan ya kirayi mutanen Kano su zama masu bin doka

Gwamnan ya kirayi mutanen jihar da su zama masu bin doka da kuma sanar da jami'an tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba don daukar mataki, The Sun ta tattaro.

Dan NNPP Onarabul Falgore Ya Zama Shugaban Majalisa a Kano

A wani labarin, an zabi Isma'il Jibrin Falgore a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Kano.

Falgore wanda dan jam'iyya mai mulki ta NNPP ce da ke wakiltar mazabar Rogo da ke jihar.

Dan majalisar ya kasance shugaban majalisar ba tare da wata adawa ba daga sauran jam'iyyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.