Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta

Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta

  • Rundunar ‘yan sandan Agbor da ke Jihar Delta sun kama Blessing Ndidi, bisa zarginta da yunkurin yanke wa mijinta mazakuta
  • Kamar yadda bayanai suka nuna, sai da ta bari ya sha giya ya yi tatil sannan ta kai masa farmakin, daga nan aka zarce da shi asibiti
  • Kakakin ‘yan sandan ya nuna yadda mijin ya ki basu hadin kai wurin gudanar da binciken yayin da ya ke kokarin rufa wa matarsa asiri

Jihar Delta - Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Agbor a Jihar Delta sun yi ram da wata Blessing Ndidi, matar auren da ta yi yunkurin yanke mazakutar mijinta, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda bayanai suka nuna tana zarginsa da rashin kamun kai ne a garin Alisemein da ke karamar hukumar Ika ta kudu cikin jihar.

Kara karanta wannan

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta
Yan sanda sun gurfanar da matar aure kan zargin yunkurin datse mazakutar mijinta. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nigerian Tribune ta tattaro bayanai akan yadda Ndidi ‘yar asalin Akokwa da ke Jihar Imo ta dade tana ji wa mijinta raunuka.

Ba wannan bane harin farko da ta fara kai masa

A daren da wannan lamarin ya faru, an samu bayanin yadda mijin nata, wanda birkila ne ya sha giya ya yi tatil kafin ta kai masa harin.

Bayan harin, an yi gaggawar zarcewa dashi wani asibitin kudi da ke Boji Boji Owa a karamar hukumar Ika ta arewa inda ake kulawa da lafiyarsa.

Rahoton ya nuna cewa matar da mijin sun kai shekaru uku da aure ba tare da haihuwa ba, kuma ta dade tana zarginsa da rashin kamun kai.

An bayyana yadda a baya ta sha kai masa hari da wuka da tabarya, tana jan kunnensa akan cewa za ta datse mazakutarsa duk lokacin da ta gane cewa yana da da tare da wata matar ta daban.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Mijin ya ki ba ‘yan sanda hadin kai wurin bincike

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace mutumin ya ki ba su hadin kai wurin binciken.

Kamar yadda tabbatar, mutumin yana kada baki ya ce:

“Ban son a zarge ta da wani abu saboda matata ce.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel