Ku Kiyayi Shan Magungunan Ƙarfin Mazakuta, Za Su Iya Kashe Ku, Shugaban NAFDAC Ta Gargaɗi Maza

Ku Kiyayi Shan Magungunan Ƙarfin Mazakuta, Za Su Iya Kashe Ku, Shugaban NAFDAC Ta Gargaɗi Maza

  • Hukumar kula da magunguna da abinci ta Najeriya, NAFDAC ta gargadi maza kan amfani da magungunan kara karfin maza
  • Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce mafi yawancin maganin karfin maza ta haramtattun hanya ake shigowa da su kuma ba su da rajista
  • Shugaban na NAFDAC ta kara da cewa yawaita amfani da magungunan na iloli ka dan adam kuma kan iya janyo matsaloli kamar hawan jini har ma mutuwa

An gargadi maza su dena amfani da magungunan kara karfin mazakuta da aka fi sani da maganin karfin maza domin cigaba da amfani da su na iya janyo bugun zuciya ko mutuwar gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

A sakon ta na Kirsimeti da sabon shekara ga ƴan Najeriya, Shugaban hukumar kula da magunguna da abinci, NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce mafi yawancin magungunan kara karfin mazan shigo da su ake yi ta haramtattun hanya.

Kara karanta wannan

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza Za Su Iya Halaka Ku, Shugaban NAFDAC Ta Gargadi Mazan Najeriya
Shugaban NAFDAC ta gargadi maza kan amfani da magungunan karfin kara karfin maza. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Magungunan ƙara ƙarfin maza ana amfani da su ne domin ƙara daɗin kwanciya tsakanin masoya kamar yadda Leadership.

A wani nazari da aka yi kan magungunan a Birtaniya, kashi 3 cikin 100 na maza 12,000 sun yi amfani da maganin (Viagra) a watanni 6 da suka wuce ba tare da izinin likita ba.

Alkaluma a Najeriya sun nuna cewa mutane na kara neman magungunan na kara karfin mazakuta.

Nazari sun nuna cewa ana amfani da waɗannan magungunan ne don ƙara tsawon lokacin jima'i, kara ni'ima tsakanin masoya yayin kwanciya da sauransu.

Wasu kuma na amfani da su ne domin maganin rashin karfin gaba da shan giya wasu kwayoyin suka janyo musu.

A cikin sanarwar da MAFDSC ta fitar a ranar Lahadi, Farfesa Adeyeye ta koka kan yadda maza da yawa suka mutu yayin amfani da magungunan kara karfin maza kuma yan uwansu su rika zargin asiri aka yi musu.

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

Farfesa Adeyeye ta ce:

"Mutane da yawa ba su san hatsarin da ke tattare da amfani da magungunan kara ni'imar jima'i ba bisa ka'ida ba ko magunguna marasa rajista."

Bugu da ƙari, ta jadadda cewa akwai ka'idojin kerawa, siyowa, talla da amfani da irin wannan magungunan.

A cewar ta:

"Yawan amfani da magungunan ƙara ƙarfin mazan na iya janyo abubuwa da dama a jikin mutum, tana mai cewa suna iya janyo hawan jini."

Ta ce idan zuciya ya dade yana buga jini zuwa wani sashi na ciki fiye da lokacin da ya kamata, suna janyo a samu karancin jini zuwa sauran sassan jikin.

Shugaban na NAFDAC ta ce hukumar ta kama a ƙalla trela 20 dauke da magunguna da abinci haramtattu da kudinsu ya kai Naira biliyan 3 a yayin kasuwar baje koli na Legas.

Bidiyon matar da ta isa wurin bikin murnar cikarta shekaru 50 a akwatin gawa ya janyo surutai

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Ranar haihuwar mutum rana ce mai ban sha’awa da birgewa a rayuwar dan Adam kuma wannan matar ta nuna wa duniya cewa ba za ta taba mantawa da ranar ba.

Matar ta zama abar caccaka da surutai a ranar shagalin cikarta shekaru 50 da haihuwa bisa yadda ta bayyana a wurin bikin cikin wani akwatin gawa na gilashi.

A bidiyon wanda shafin @gossipboyz1 su ka wallafa a Instagram, an ga yadda ta isa wurin a cikin akwatin gawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel