Gwamnatin Jihar Ogun Ta Ankarar da Mutane Bayan Bullar Cutar Kwalara A Wasu Yankuna

Gwamnatin Jihar Ogun Ta Ankarar da Mutane Bayan Bullar Cutar Kwalara A Wasu Yankuna

  • Gwamnatin jihar Ogun ta tabbatar da bullar cutar Kwalara a karamar hukumar Ijebu ta Arewa da ke jihar
  • Hadimar gwamnan a bangaren lafiya, Dakta Tomi Coker ita ta sanar da haka a yau Lahadi 17 ga watan Satumba
  • Coker ta shawarci jama’a da su kiyaye lafiyarsu da kuma na muhallinsu wurin tabbatar da wanke hannayensu

Jihar Ogun – Gwamnatin jihar Ogun ta ankarar da mutane kan bullar cutar Kwalara a karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimirsa a harkar lafiya, Dakta Tomi Coker ta fitar a yau Lahadi 17 ga watan Satumba.

Gwamnatin jihar Ogun ta shawarci jama'a kan cutar kwalara
Gwamnatin Jihar Ogun Ta Yi Martani Kan Bullar Cutar Kwalara. Hoto: @dabiodunMFR.
Asali: UGC

Meye gwamnatin Ogun ke cewa kan kwalara?

Coker ta bayyana Kwalara a matsayin cutar da ke yaduwa a lokacin damuna da kuma rashin tsafta na muhalli, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da gaske sojoji sun kwace mulki a kasar Kongo? Mun binciko muku gaskiyar batu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce:

“Yawanci cutar na zuwa ne da gudawa wani lokaci da amai wanda ke jawo rashin karfin jiki.
“Kwalara na iya yin sanadin rayuwar mutum musamman idan ba a dauki mataki kwakkwara ba.”

Hadimar gwamnan ta bai wa jama’a shawara da su kai duk wani rahoton gudawa da su ka samu ko da amai ko babu ga asibitoci mafi kusa da su.

Ta kuma ya shawarci jama’a da su kula da kiyaye lafiyar su ta hanyar wanke hannayensu a duk lokacin da su ka shiga bandaki da kuma lafiyar muhalli.

Wane shawara ta bayar kan cutar kwalara?

Ta bukaci mutanen jihar gaba daya da su tabbatar sun yi amfani da ruwa mai tsafta ko kuma su tsaftace shi kafin amfani da shi wurin dafa abinci da wanke kwanuka.

Dakta Tomi ta bayar da lambar waya na wakili a karamar hukumar da za a kai rahoton irin wannan matsalar a asibitoci na kusa da jama’a, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shara ta kare a Kano, Abba Gida-Gida ya dauki ma'aikatan tsaftace birni mutum 4500

Ta kara da cewa:

“Ya kamata mu kiyaye yin ba haya a fili kuma mu zama masu taka tsan-tsan wurin sanin abincin da za muke ci da kuma ruwan sha.
“Babban abin da ke jawo Kwalara shi ne lokacin ruwan sha ko abinci ya hadu da ba haya ta hanyar da ba ta dace ba.”

Babbar Mota Ta Hallaka Mata Mai Ciki A Ogun

A wani labarin, Wata babbar mota ta yi ajalin wata mata mai ciki yayin da ta kusa cikin kasuwa a karamar hukumar Obafemi Owode da ke jihar Ogun.

Rahotanni sun a tattaro cewa motar ta rasa birki ne yayin da direban ya gagara shawo kan motar inda hakan ya yi sanadin matar da yaronta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel