Masana’antu: Dangote Ya Samu Sabon Matsayi a Cikin Manyan Attajiran Duniya

Masana’antu: Dangote Ya Samu Sabon Matsayi a Cikin Manyan Attajiran Duniya

  • Attajirin Najeriya da Afrika, Aliko Dangote, ya doke attajirai 19 domin zama na shida a jerin masu masana'antu mafi arziki a duniya
  • Shugaban rukunin Dangote ya mallaki kamfanin siminti, matatar mai, da kamfanin taki, inda ya mallaki 85% na hannayen jarinsu
  • An fitar da sabon jadawalin ne a dai dai lokacin da aka ruwaito faduwar darajar Naira ta lakume $2.6bn daga dukiyar Dangote

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Duk da asarar $2.6bn a watan Afrilun 2024 sakamakon faduwar Naira, hamshakin attajirin Nigeria da Africa, Aliko Dangote, ya kasance a matsayi na shida a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a masana’antar kere-kere.

Sabon matsayin Aliko Dangote a cikin manyan attajiran masu kamfanoni
Aliko Dangote, ya zama na 6 a jerin attajiran masu kamfanoni a duniya. Hoto: Dangote Industries.
Asali: Facebook

Aliko Dangote shi ne shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya mallaki kamfanin siminti, matatar mai, da kamfanin taki, inda aka ce ya mallaki kashi 85% na hannayen jari a kamfanonin.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Dangote ne kadai dan Africa a jadawalin

Insidermonkey.com, wani kamfani na Amurka, ya aiwatar da wannan kididdigar ta hanyar amfani da tsarin tantance karfin kamfanonin, hada-hadar kudadensu, yawan jarin da aka zuba da sauran matakai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hamshakin attajirin na Najeriya shi ne kadai dan Afirka a cikin wannan jadawalin na attajirai 25 mafi arziki a masana’antar kere-kere.

A wani rahoto makamancin wannan da mujallar CEOWorld ta fitar a shekarar da ta gabata, Dangote ya rike matsayi na 9 a jerin attajirai 10 da suka fi kowa kudi a masana’antu a duniya.

Manyan attajiran 'yan kasuwa guda 5

1. Reinhold Wuerth

A cewar rahoton africa.businessinsider, Reinhold Wuerth ne a lamba ta daya a jerin attajirin da suka fi kowa kudi a masana'antar kere-kere, yana da zunzurutun kudi har dala biliyan 35.3.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ki daukar matsaya kan harajin tsaron yanar gizo, 'dan majalisa ya koka

2. He Xiangjian

He Xiangjian na kasar China ya zo na biyu a jerin attajiran bayan da ya tara dukiyar da darajarta ta kai dala biliyan 26.1.

3. Michael Hartono

Babban dan kansuwa a uku a cikin jerin shine Michael Hartono, wanda ke da dukiyar da ta kai dala biliyan 23.1.

4. Takemitsu Takizaki

Takemitsu Takizaki na kasar Japan ya zama dan kasuwa na hudu mafi arziki a duniya, wanda ya mallaki dala biliyan 20.7.

5. James Ratcliffe

Kamar yadda jadawalin ya nuna, James Ratcliffe shine dan kasuwa na biyar mafi arziki a duniya bayan da ya mallaki dala biliyan 16.2.

Dangote zai gina kamfani a Gombe

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa attajirin dan kasuwa Aliko Dangote, ya sanar da shirinsa na gina kamfanin siminti a jihar Gombe.

Ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan ganawar sirri da ya yi da gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.