Babbar Mota Ta Hallaka Mata Mai Ciki Yayin Da Ta Kusa Cikin Kasuwa A Jihar Ogun

Babbar Mota Ta Hallaka Mata Mai Ciki Yayin Da Ta Kusa Cikin Kasuwa A Jihar Ogun

  • Jimami yayin da babbar mota ta murkushe mata mai ciki da yaro dan shekara biyu a karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun
  • Direban babbar motar ya gagara shawo kan motar yayin da birkinta ya tsinke tare da hallaka matar a cikin kasuwa
  • Kakakin hukumar kula da hadura, FRSC a jihar, Florence Okpe ta bayyana cewa su na dakon rahoto daga jami'ansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Wata babbar mota ta murkushe mata mai ciki da raunata yaronta mai shekaru biyu a karamar hukumar Obafemi Owode da ke jihar Ogun.

Punch ta tattaro cewa direban motar ya gagara shawo kan motar bayan birki ya balle inda ya kutsa cikin kasuwa, Legit.ng ta tattaro.

Mota ta murkushe mata mai ciki a Ogun
Hukumar FRSC ta tabbatar da mutuwar mata mai ciki a Ogun. Hoto: FRSC.
Asali: Facebook

Meye ya jawo hatsarin motar a Ogun?

Motar ta kuma mutssuke karamar mota da babur a kasuwar inda direban ya tsere bayan faruwar hatsarin saboda gudun fushin jama'a.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar mai ciki ta zo siyan kayayyaki ne cikin kasuwar lokacin da abin ya faru, cewar Premium Times.

Wani wanda bai so a bayyana sunansa bayyana cewa:

"Matar mai ciki na daya daga cikin wadanda ta fara ganin motar ta nufo cikin kasuwar.
"Matar ta mai ciki ta so ta gudu tare da karamin yaronta amma doguwar rigar da ta saka ta kawo mata cikas inda ta fadi kasa motar ta bi ta kanta."

Meye hukumar FRSC ta ce kan hatsarin a Ogun?

Yayin da ya ke martani, kakakin hukumar FRSC, Florence Okpe ya ce su na jiran rahoton jami'ansu bayan kammala aikin ceto.

Ya ce:

"Jami'an mu za su ba mu rahoto da zarar sun kammala aikin ceto a wurin da abin ya faru."

Matashi ya kulle iyayensa a daki, ya sace motarsu

Kara karanta wannan

Abin Tausayi Yayin Da Uwa Ta Kona Dan Cikinta Da Ruwan Zafi Kan Zargin Neman Mata, Bayanai Sun Fito

A wani labarin, wani matashi mai shekaru 17 ya fakaici iyayensa tare da tafka musu mummunan sata a jihar Ogun bayan ya kulle su a daki.

Matashin mai suna Ayomiposi Esan ya sace wayoyin salula 3 da janareta 2 da kuma mota kirar Toyota Corolla na iyayen nasa.

Esan ya kulle iyayen nasa a daki tare da danna musu kwado lokacin da su ke bacci inda ya kwashe musu kayayyaki da dama a gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel