Jajirtaccen Shugaba: Yadda Shugaban Kasar Amurka ya Jinjinawa Tinubu a Indiya

Jajirtaccen Shugaba: Yadda Shugaban Kasar Amurka ya Jinjinawa Tinubu a Indiya

  • Joe Biden ya yaba da kokarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wanda ya karbi mulki a watan Mayu
  • Abin da Shugaban Najeriya yake yi a bangaren tattalin arziki ya burge abokin aikinsa na Amurka
  • Fadar shugaban Amurka ta fitar da jawabin shugaba Biden a lokacin da ake taron G20 a kasar Indiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

India - A ranar Lahadi, Joe Biden ya tofa albarkacin bakinsa game da yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya da musamman ECOWAS.

A wani jawabi da ya fito daga fadar shugaban Amurka, an ji Joe Biden ya na yabawa irin kokarin da takwaransa na Najeriya yake yi tun da ya shiga ofis.

Kokarin da Bola Ahmed Tinubu yake yi na tabbatar da tsarin damukaradiyya a kasar Nijar da aka kifar da gwamnatin farar hula ya burge kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a G20 Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Tinubu: Jawabin fadar White House

Biden ya yi maraba da gwamnatin Tinubu wajen kawo sauyi a bangaren tattalin arziki kuma ya godewa Tinubu na jajirtaccen shugabancin da ya nuna a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS na tabbatar da damukaradiyya da doka a Nijar da fadin yankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- White House

Rikicin ECOWAS da kasar Nijar

Da ya zauna da mataimakin ministan harkokin Afrika na Amurka, shugaba Tinubu ya fadawa Molly Phee hikimar yakar gwamnatin sojojin Nijar.

The Cable ta ce Tinubu ya ce ya zama dole ayi amfani da karfin bindiga a Jamhuriyyar kasar Nijar idan ta kama domin tabbatar da tsaro.

Biden yake cewa Najeriya ta na kan gaba a tsarin mulkin farar hulda karfin tattali a duk Afrika.

Me ya kai Tinubu taron G20?

Channels ta ce shugaban na Amurka ya yi bayanin dalilin gayyato Najeriya da aka yi zuwa taron G20 da aka yi a birnin New Delhi a kasar Indiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN, EFCC, Hafsun Soji da Mutanen Buhari da Tinubu Ya Kora a Kwana 100

Gayyatar Najeriya zuwa taron G20 dalili ne na girmama rawar da ta ke takawa a duniya a matsayin babbar jagorar damukaraddiya da tattalin arzikin Afrika

Dangiwa Umar ya soki Buhari

Rahoto ya zo cewa Kanal Dangiwa Umar ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yaudari jama’a, kuma ya na sane da satar da aka yi a mulkinsa.

Sojan ya ce maganar gaskiya ita ce Muhammadu Buhari ya jagoranci gwamnatin da ta fi kowace barna musamman ta ofishin Gwamnan bankin CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel