Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Mukaddashin Shugaban Hukumar FIRS

Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Mukaddashin Shugaban Hukumar FIRS

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada minsta Zacch Adedeji a matsayin mukaddashin shugaban hukumar tara kudin haraji ta kasa (FIRS).

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon mukaddashin shugaban na FIRS.

Zacch Adedeji ya zama mukaddashin shugaban hukumar FIRS
Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Mukaddashin Shugaban Hukumar FIRS Hoto: Punch
Asali: UGC

Jerin abubuwa 12 game da sabon mukaddashin hukumar FIRS

1. Mista Zacch A. Adedeji ya fito daga jihar Oyo kuma ya kasance mai ba Tinubu shawara ta musamman kan kudaden shiga.

2. Ya kasance kwamishina a gwamnatin marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abila Ajimobi yana da shekaru 33 a lokacin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. Adedeji ya fito daga yankin Iwo-Ate a karamar hukumar Ogo-Oluwa ta jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar FIRS

4. Ya karancin bangaren lissafin kudi sannan ya kammala karatunsa da digiri mafi daraja a jami'ar Obafemi Awolowo.

5. Ya kuma yi digirinsa na biyu a jami'ar Obafemi Awolowo.

6. A kwanan nan ne ya kammala digirinsa na uku a bangaren hada-hadar kudi a jami'ar Obafemi Awolowo.

7. Adedeji ya kasance mamba a cibiyar ICAN da Cibiyar Haraji ta Najeriya (CITN).

8. Ya kasance tsohon dalibi na Makarantar Gwamnati ta Harvard Kennedy.

9. Har ila yau, ya kasance tsohon Manajan Kamfanin Procter & Gamble (P&G).

10. Tsohon kwamishinan kudi ne a jihar Oyo.

11. Adedeji ya kasance tsohon babban sakatare na hukumar ci gaban sukari ta kasa (NSDC).

12. Zai karbi mulki daga Mohammed Nami wanda wa'adinsa a matsayin shugaban FIRS zai kare a watan Disambar 2023.

Shugaba Tinubu ya sa labule da Ganduje da hafsoshin tsaro a Villa

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tawagar wakilai ƙarƙashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje a fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Karin Kwamishinoni 10, Ya Aike da Saƙo Ga Majalisa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa taron, wanda aka shiga da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin yau Alhamis, ya samu halartar hafsoshin tsaron ƙasar nan.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa har zuwa loƙacin haɗa wannan rahoton, ba bayyana ajendar da taron zai maida hankali ba.

Duk da haka, wasu rahotanni sun bayyana cewa tawagar wakilan zata gabatar wa shugaban ƙasa kundin da ke kunshe da hanyoyin warware rikicin manoma da makiyaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng