Maltina: An bude katafaren wajen koyon sana'a a jihar Kaduna
Shahararren kamfanin Nigerian Breweries – ya kaddamar da wata cibiyar koyon sana'o'i ta zamani da aka sanya wa suna Maltina a Kakuri, Kaduna, a wani bangare na kokarinsa na inganta rayuwar al’umma.
A lokacin bikin kaddamar da wajen koyon sana'ar, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe, ta bayyana shirin a matsayin gagarumin ci gaba da zai samar da damammaki, inganta rayuwa da hanyoyin bunkasa tattalin arziki ga matasa da dama a fadin jihar.

Asali: UGC
Mataiamkiyar gwamnan ta ce:
"Cibiyar koyon sana'ar tana da tasiri sosai. Yayin da matasa za su samu kwarewa da damar dogaro da kai a fannin tattalin arziki, za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin mu na gida, su karfafa al’ummominsu, tare da zaburar da wasu su ma su bi irin wannan hanya ta ci gaba da dogaro da kai."

Asali: UGC
Yayin da take nuna matukar godiya ga shugabancin kamfanin bisa wannan kyakkyawan aikin taimakon jama'a, Hajiya Balarabe ta ce cibiyar tana nuna irin kudurin kamfanin na dorewar ci gaba da sadaukar da kai ga jin dadin al’ummomin da yake aiki a cikinsu.
Ta kara da cewa:
"Aikin da Nigerian Breweries ta yi a nan ya dace da manufofin gwamnatin Sanata Uba Sani. Gwamnatin jihar Kaduna ta fahimci muhimmancin koyon sana’o’in zamani musamman a fannin Fasaha da Sadarwa (ICT) da sauran muhimman sana’o’i.
"Wannan cibiya za ta taka rawar gani wajen sauya masu neman aiki su zama masu samar da aiki, wanda hakan zai kara yawan masu dogaro da kai da rage rashin aikin yi a jiharmu."
Ta kuma bayyana aniyar gwamnati na ci gaba da samar da ingantaccen yanayi ga kamfanoni masu zaman kansu da 'yan kasuwa domin su bunkasa tare da ba da gudunmawa ga ci gaban Kaduna.

Asali: UGC
Shi ma a nasa jawabin, Manajan Nigerian Breweries, Hans Essaadi, ya bayyana kaddamar da aikin a matsayin wata babbar nasara a tafiyar kamfanin na tabbatar da dorewar ci gaba da karfafa tattalin arziki.
Essaadi ya ce wannan aikin shaida ne ta yadda kamfanin ke sadaukar da kai wajen kyautata rayuwa da gina al'umma, musamman ga matasa da matan unguwar Kakuri.
Ya bayyana cewa an gina cibiyar ne domin dacewa da halin da duniya ke ciki na mayar da kwarewa a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arziki.

Asali: UGC
Essaadi ya ce:
"Rashin aikin yi da gaza samun isasshen aiki na daga cikin manyan kalubale, musamman ga matasa da mata.
"Wannan cibiya za ta magance wadannan matsaloli ta hanyar ba wa mutane horo da dabarun sana’o’i masu amfani.
"Za ta karfafa dogaro da kai, habaka kasuwanci, da kuma taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin yankin."
A cewarsa, cibiyar za ta ba da horo a fannoni daban-daban kamar dinki, kera takalma, girki, gyaran gashi, fasahar ICT da sauran sana’o’i da za su taimaka wajen dogaro da kai.
Ya kuma bukaci wadanda za su ci gajiyar shirin da su amfana da damar domin kawo sauyi a rayuwarsu wajen ci gaba da bunkasa tattalin arzikinsu.
A nasa bangaren, Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, wanda mai unguwan Makera, Alhaji Shehu Tijani ya wakilta, ya jinjinawa kamfanin bisa goyon bayan da ya dade yana bai wa al’umma tsawon shekaru fiye da 60 ta hanyar taimaka wa matasa da mata da kuma wasu manyan ayyuka ciki har da gina cibiyar.

Asali: UGC
Mai martaba Ahmed Bamalli ya godewa kamfanin bisa kulla kyakkyawar alaka tsakaninsa da al’ummar yankin, inda ya ce matasa da mazauna yankin da dama sun taba amfana da irin wannan kokari ta hanyar samun dama koyon sana'a da daukar nauyin gasar karatun Alkur'ani da sauransu.
Daga karshe, ya roki shugabannin kamfanin da su ci gaba da tallafawa tafiyar da cibiyar ta hanyar bayar da kulawar da za ta tabbatar da ci gaba da inganta kayayyakin cibiyar.
Asali: Legit.ng