“Ba Zan Jira Gwamnatin Tarayya Ta Gyara Hanyoyin Da Suka Lalace a Jihata Ba”, Gwamnan Jihar Neja

“Ba Zan Jira Gwamnatin Tarayya Ta Gyara Hanyoyin Da Suka Lalace a Jihata Ba”, Gwamnan Jihar Neja

  • Gwamnatin Mohammed Umar Bago na jihar Neja ta kaddamar da aikin fara gyara hanyoyi a fadin jihar
  • Gwamna Bago ya ce ba za su jira sai gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta zo ta gyara hanyoyin tarayya da ke jihar ba
  • A cewarsa za su nemi a dawo masu da abun da suka kashe idan aka kammala aikin gyare-gyaren titunan
  • Legit Hausa ta zanta da wasu mazauna garin Minna don jin ta bakinsu kan halin da titunan garin ke ciki

Jihar Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana cewa daga yanzu jihar ba za ta sake jiran gwamnatin tarayya ta zo ta gyara hanyoyinta da suka lalace a fadin jihar ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya bayyana cewa gwamnatin za ta nemi a biya ta abun da ta kashe idan aka kammala gyaran hanyoyin, yana mai cewa yanayin da hanyoyin tarayya ke ciki a jihar ba abu ne da za a iya bari ba a yanzu saboda rashin samun martani daga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Koka, Ya Ce 'Yan Bindiga Sun Mamaye Jiharsa

Gwamnan Neja ya ce zai fara gyaran tituna
“Ba Zan Jira Gwamnatin Tarayya Ta Gyara Hanyoyin Da Suka Lalace a Jihata Ba”, Gwamnan Jihar Neja Hoto: Mohammed Umar Bago
Asali: Facebook

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da aikin gyara da shimfida titunan garin Minna, Bago ya ce:

“Jahar Neja ita ce jiha mafi girma ta bangaren yalwar filaye kuma ita ce ta fi kowacce jiha yawan hanyoyin tarayya. Ba za mu kara jiran gwamnatin tarayya ta yi mana hanyoyin ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna tattaunawa da fadar shugaban kasa don ganin yadda za mu nemi a dawo mana da kudaden ayyukan da muke yi amma duk da haka, za mu ci gaba da aikin hanyoyin."

Gwamnan Neja zai shimfida tituna a fadin jihar

Gwamnan ya kuma bayyana cewa nan da shekaru hudu masu zuwa jihar za ta gyara tare da shimfida tituna masu tsawon kilomita 1,500 a fadin jihar, inda ya ayyana fadada kofofin birnin Minna da tsawon kilomita 22 don mayar da masarautar Minna kilomita 100.

Kara karanta wannan

Tsadar Fetur: Daga Dawowa Yajin Aiki, Ma’aikata Su na Tunanin Sake Rufe Ko Ina

Ya bayyana cewa akwai tituna 556 da ake shirin sabonta su a shekaru hudu masu zuwa yayin da gwamnati ke shirin kashe Naira tiriliyan 1 kan ababben more rayuwa a shekaru biyu masu zuwa.

Bago ya bukaci matasa da su yi amfani da damar shirin zuba jari da sabunta birane da gwamnatin ke yi yana mai bayyana tsare-tsaren gwamnati na tallafawa masu kananan sana'o'i a fadin jihar.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Suleiman Umar ya bayyana cewa hanyoyin masu nisan kilomita 202 na garin Minna za su hada da gyaran tituna 14 da ake da su, da gina sabbin tituna guda takwas, da gadar sama guda biyar yayin da za a mayar da tituna masu hanya daya zuwa biyu.

Ya bayyana cewa koda dai wannan ne babban aikin sabunta birane da jihar ta taba yi, amma abu ne da za a iya zimmawa.

Martanin mazauna garin Minna kan shirin gyara tituna da gwamnati ke shirin yi

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Legit Hausa ta zanta da wasu mazauna garin Minna don jin halin da hanyoyin jihar ke ciki inda suka koka da lamarin.

Malam Hassan Abubakar ya ce matakin da gwamnatin jihar ke shirin dauka na aiwatar da ayyukan ba tare da ta jira gwamnatin tarayya ba shine daidai domin dai hanyoyin na bukatar agajin gaggawa.

Ya ce:

“Na ji dadin wannan mataki da gwamnatin Bago ke shirin dauka domin dai hanyoyinmu na cikin halin wayyo Allah, ba ga na cikin garin Minna ba, ba ga sauran hanyoyin ba.
“Kada ma dai hanyar Bida zuwa Minna ya ji labari. Gaba daya hanyar babu kyau, tafiyar Minna zuwa Bida da bai fi ya dauki mutum mintuna 45 zuwa awa daya ba sai ka shafe awanni biyu zuwa biyu da rabi kana abu daya.

A nasa bangaren, mallam Abdulhameed kuwa cewa ya yi ya ga an fara ajiye kayan aiki a wajen Shiroro Otel.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Kawo Motocin Da Za Su Rika Daukar Mutane Kyauta Saboda Tsadar Fetur

“Na je wucewa a wajen Shiroro otel na ga manyan motocin aiki da injiniyoyi da kuma leburori sun taru ga dukkan alamu dai suna tattauna yadda za a tafiyar da aikin ne. Wannan aikin gyara tituna da gwamnan ke yi ci gaba ne mai kyau don gaskiya titunanmu na bukatar gyara.
“A ce ka shigo cikin babban birnin jiha wato Minna amma sai ka ga duk titunan cikin gari a yanke ko’ina ka bi tudu da kwari ne.”

Kamfanin Wutar Lantarki Ya Sanar Da Gyara Wutar Lantarki A Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa bayan shafe fiye da sa'o'i 12 babu wuta a fadin Najeriya baki daya, yanzu wutar ta dawo.

Wannan na zuwa bayan dauke wutar a fadin kasar baki daya wanda aka shafe kusan shekara ba a samu irin haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng