“Yana Jin Kunci Da Kuke Ciki”: Wike Ya Magantu a Kan Tanadin Da Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya

“Yana Jin Kunci Da Kuke Ciki”: Wike Ya Magantu a Kan Tanadin Da Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya

  • Nyesom Wike ya aika gagarumin sako ga yan Najeriya dangane da babban shirin da gwamnati mai ci ke yi
  • Ministan birnin tarayyar ya roki yan Najeriya da su kara hakuri da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya jaddada cewar ajandar kawo sauyi na APC na nan daram dam, yana mai cewa Tinubu na nufin yan Najeriya da alkhairi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sake ba yan Najeriya tabbaci kan jajircewar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cika alkawaran zabensa.

Wike ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu na nufin yan Najeriya da alkahiri
“Yana Jin Radadinku”: Wike Ya Magantu a Kan Tanadin Da Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike ya bayar da tabbacin ne a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, yayin kaddamar da aikin gyara tituna a yankin Garki da ke Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa Tinubu na nufin yan Najeriya da alkhairi kuma cewa ajandarsa na sabonta fata shine kan gaba a cikin abun da shugaban kasar ya sa a gaba, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

“Idan Lasifika Ba Zai Yi Aiki Ba, Ta Yaya Abuja Za Ta Yi Aiki”: Wike Ya Yi Wa Jami’an FCTA Wankin Babban Bargo

Dan siyasar ya roki yan Najeriya da su yarda gwamnati mai ci da marawa kyakkyawar nufinta baya, yana mai cewa Tinubu na jin radadinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Karamar ministar birnin tarayya da ni kaina mun kasance a nan don ba ku tabbacin cewa ajandarsa (Tinubu) na sabonta fata na aiki da kuma sanar da ku birnin tarayya na aiki. Ajandar mai girma shugaban kasa ba wai maganar fatar baki bane kawai (yana a aikace). Kuma wannan ne dalilin da yasa muka zo don fara kaddamar aikin wasu hanyoyi a yankin nan," Wike ya fada ma taron jama'a.

Wike, wanda ya koka da yanayin ababen more rayuwa da sauransu a babban birnin tarayyar Najeriya, ya ba mazauna Abuja tabbacin cewa gwamnatinsa za ta inganta birnin tarayyar.

"Birnin tarayya kafin yanzu ba daya take birnin tarayya a yanzu ba. Za mu sauya komai," in ji shi, yana mai neman mazauna yankin da su marawa gwamnati baya da kara hakuri.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Wike ya caccaki ma'aikatan hukumar FCTA

A wani labarin, mun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi wa jami'an hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) wankin babban bargo.

Wike ya caccaki jami'an hukumar kan gazawarsu wajen shirya taro mara tangarda yayin kaddamar da aikin gyaran wata hanya a Abuja a ranar Litinin 11 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel