Yayin Da Ake Bin Najeriya Bashin Tiriliyan 87, Tinubu Ya Gaza Biyan China Da Sauran Kasashe A 2023

Yayin Da Ake Bin Najeriya Bashin Tiriliyan 87, Tinubu Ya Gaza Biyan China Da Sauran Kasashe A 2023

  • Najeriya ta gaza biyan kasar China basukan da ta ke binta a zango na biyu na shekarar 2023
  • Bincike ya tabbatar da cewa Najeriya ta iya biyan basukan ne ga hukumomi biyu kacal a lokacin da ake maganan
  • Kasar China kadai na bin Najeriya bashin da ya kai Dala biliyan 4.34 har zuwa watan Yunin wannan shekara da mu ke ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa ana bin Najeriya bashin fiye da Naira tiriliyan 87 a karshen watan Yuni na 2023.

Bashin kamar yadda Hukumar Gudanar da Bashi (DMO) ta tabbatar ya karu zuwa tiriliyan 87 ne daga 49.89 a watan Disambar 2021.

Tinubu ya gaza biyan basukan Najeriya a 2023
Halin da Tinubu ke ciki na biyan basuka a Najeriya. Hoto: State House.
Asali: Facebook

Meye aka ce kan bashin da Tinubu zai biya?

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta tabbatar da shi a yanar gizonta.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce jimillar kudaden da ake bin kasar gida da waje wanda ya hada da jihohi 36 da birnin Abuja ya kai Naira tiriliyan 87.739.

Punch ta tattaro cewa bashin da Bankin CBN kadai ke bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 22 wanda ke cikin bashin cikin gida.

Legit ta tattaro cewa bashin kasar ya kai Dala miliyan 22.8 a zango na biyu na shekarar 2023.

Wani malamin tattalin arziki, Lamido Bello ya ce bashin Najeriya ya na matukar gurgunta tattalin arzikin kasar.

Ya ce:

"Mu na karbo bashi amma mu na kashe su ta wasu hanyoyi madadin manya-manyan ayyuka ba, wannan shi ne babbar matsalar."

Har ila yau, Yusuf A. Aliyu wanda dalibi ne a tsangayar tattalin arziki ya bayyana cewa wannan ba abin damuwa ba ne saboda kasashe da dama na dauke da nauyin basuka.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Amma ya yi fatan cimma kudirin da Tinubu ya yi na rage biyan basukan da kudaden shiga kamar yadda sauran gwamnatocin su ka yi.

Yadda Najeriya ta gaza biyan basuka a 2023

Hukumar DMO ta ce Najeriya ta biya Dala miliyan 21 ga Kungiyar Cigaban Kasa da Kasa (IDA) da kuma Dala miliyan 1.9 ga Bankin Raya Musulunci a watan Yunin 2023.

Kasashe biyar na bin kasar kudin da ya kai Dala biliyan 5.16 da su ka hada da Faransa da China da Indiya da Jamus da kuma Japan.

Har ila yau, Najeriya ta samu nasarar biyan Dala biliyan 1.17 na basukan ketare a farkon shekarar 2023.

Yawan kudade da kasashen da ke bin Najeriya bashi

A wani labarin, Bankin Duniya a ranar Litinin 26 ga watan Yuni ta sanar da cewa ta amince da ba wa Najeriya sabon bashi na $500m.

A cikin sanarwar da bankin ta fitar, ta ba da bashin ne saboda inganta rayuwar mata a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel