Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

Alakar kudi a matsayin kadarar musaya mai daraja ya ta'allaka da yadda al'umma ke mu'amalantarsu, a Najeriya ma, batun bai sauya zane ba.

Zai baku sha'awa da matukar burgewa ku san yadda ake hada-hada a shekarun da suka gabata a Najeriya ba tare da kudin takarda ko tsaba ko sulalla ba, da kuma yadda lamarin ya sauya zuwa yanzu.

A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro daga Babban Bankin Najeriya abubuwan da ake huldar cinikayya dasu kafin zuwan kudin takarda da sulalla ko tsaba da kuma yadda aka samar da kudaden da muke kashe wa yanzu.

Waiwaye: Tarihin kudaden Najeriya, lokacin da aka fara daga amfani da gishiri a matsayin kudi
Kudaden Najeriya | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

1. A da an yi cinikayya da gishiri

Za ku ji batun kamar almara, amma gaskiya ne. A cewar Babban Bankin Najeriya (CBN), kayayyaki kamarsu gishiri, kwalba ko kayan karau da sauran abubuwa sun kasance abubuwa masu daraja a madadin kudi kafin zuwan turawan mulkin mallaka.

2. Zuwan karfe; sulalla

A farkon zuwan sulalla, Bankin Ingila ke lura da su kuma ke samar dasu a matsayin wata harkalla mai zaman kanta. Wannan ya ci gaba har zuwa shekarar 1912.

Kara karanta wannan

Kudin yin waya da hawa shafin yanar gizo zai karu a Najeriya, an kawo sababbin tsare-tsare

3. Zuwan kudin takarda mallakar turawa

Kamar dai sauran kasashen Afrika ta Yamma, mafi girman kudin takarda da Najeriya ta fara mallaka shi ne fam. A bangare guda, sule kuwa shi ne mafi darajan tsaba na karfe.

4. Kudin takarda mallakar Najeriya

A shekarar 1959 Najeriya ta fara samar da kudin takarda mallakarta, duk da cewa, hakan bai gama kankama ba har sai shekarar 1962 lokacin ne kudin ya fara nuna Najeriya a matsayin jamhuriya mai 'yanci. Sabanin yanzu, a da ana rubuta Tarayyar Najeriya a jikin kudi.

5. Zuwan N1, N5 da N10

Kudin takarda a Najeriya ya fara zuwa ne cikin samfuri uku, wato; N1, N5 da N10. Hakan ya bayyana ne a ranar 2 ga watan Yulin 1978. A shekarar 1977, aka kaddamar da gudan N20.

6. Zuwan kudin leda

A ranar 28 ga watan Fabrairun 2007, N20 ta leda ta fara bayyana a Najeriya, wacce har yanzu ita ake kashe wa. Hakazalika an fitar da sabbin tsarin kudaden karfe na N1 da kwabo 50.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

7. Zuwan N50 ta leda

Yayin da Najeriya ta cika shekaru 50 da samun 'yancin kai, a lokacin ne aka fitar da sabuwar samfurin N50 ita ma ta leda kamar dai N20, a ranar 29 ga watan Satumban 2010. Daga baya kuwa aka sauya tsarin N100 ta Najeriya zuwa wani sabon tsari.

Bayani dalla-dalla: Yadda daina sayarwa yan kasuwan canji Dala zai shafi darajar Naira

A wani labarin, Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya yiwa manema labarai bayan zaman kwamitin kudi MPC na bankin ranar Talata.

Ya ce N5. 7 billion da ake baiwa yan kasuwar canji ba zai yiwu a iya cigaba ba saboda kimanin yan kasuwan canji 5500 ake baiwa $110million kowani mako.

Tun lokacin, farashin Naira ya sauka 523/$ a kasuwar bayan fagge ranar Laraba, karo na biyu bayan saukar da yayi ranar Talatar.

A rahoton da aka gani a shafin naijabdcs.com, shafin yan kasuwar Canji, an sayi Dalar Amurka a farashin N515 kuma an sayar a N523 ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.