Dalilin da Yasa Na Zabi Zuwa BUK Akan Jami’ar da Ta Min Tallan Bani Bani N20m Duk Wata, Tsohon Shugaban NUC

Dalilin da Yasa Na Zabi Zuwa BUK Akan Jami’ar da Ta Min Tallan Bani Bani N20m Duk Wata, Tsohon Shugaban NUC

  • Tsohon shugaban NUC ya bayyana cewa, an yi masa tayin albashin miliyoyin kudi, amma ya ki amsawa don ya koyar a BUK
  • Ya bayyana hakan ne a wani taro, inda yace burinsa ya ci gaba da karantarwa a BUK bayan kammala aikinsa a hukumar ta NUC
  • A tun farko, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Farfesa Rasheed a shugabancin NUC a lokacin da yake VC a BUK

Jihar Kano - Tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya bayyana yadda ya ki amincewa da tayin da wata jami’a ta yi masa na Naira miliyan 20 duk wata.

Rasheed, wanda tsohon shugaban jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ne a makon jiya ya sanar da yin murabus daga NUC da radin kansa, shekaru uku kafin cikar wa’adinsa.

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

Ya fada a fili cewa, burinsa shi ne ya ci gaba da karantarwa a BUK, kamar yadda jaridar Daily Trust a karshen mako.

Farfesa ya ce an masa tayin miliyan 20, amma ya ce BUK zai dawo
Farfesa Abubakar Adamu Rasheed | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Meye matsayinsa a baya?

Ya kasance VC a jami’ar ta BUK kafin daga bisani tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugabancin hukumar kula da jami’o’i.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da yake jawabi a wajen liyafar da jami’ar ta shirya domin yi masa maraba, Farfesa Rasheed ya ce ya bar mukamin ne don kawai ya ci gaba da koyarwa har ya kai yin ritaya.

Aikin da na fi kauna shi ne koyarwa, inji Farfesa Rasheed

Da yake jawabi, ya ce aikin da ya fi ba shi sha’awa shi ne koyarwa, don haka ya dawo jami’ar don ci gaba daga inda ya tsaya.

A cewarsa:

“Duk tsawon rayuwata, aikin da na fi so shi ne koyarwa. Amma, abubuwa kan bijiro, abubuwa suka taso da suka min barin aikin jami'a.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An ga Tsohon Shugaban Kungiyar ASUU Da Ya Bata

Hakazalika, ya bayyana yadda ya taba barin aikin a baya na tsawon shekaru shida, amma ya sake dawowa don ba da gudunmawarsa.

An min tayin miliyoyi bayan na bar NUC

Ya kuma bayyana cewa, bayan barin NUC, wata jami’a mai zaman kanta ta yi masa tayin biyansa albashin Naira miliyoyi duk wata idan ya amince zai yi aiki da ita, amma ya ki saboda burin zama a BUK.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Najeriya ke ci gaba samun kafuwar jami’o’i masu zaman kansu, Farfesa Rasheed ya ce har yanzu kasar na bukatar karin cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu don cike gurbin karatu ga dalibai duk shekara.

Ina son zama ‘Emeritus’ a BUK

A wani labarin, Abubakar Adamu Rasheed wanda ya sauka daga kujerar hukumar NUC a kan rajin kan shi, ya yi karin haske a kan hikimar barin matsayinsa.

A makon nan ne This Day ta rahoto Farfesa Abubakar Aliyu Rasheed ya na cewa ya bar NUC ne saboda ya zama Emeritus a jami’ar Bayero da ke Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 a Cikin Wata 1

Malamin makarantar ya ce da ya cigaba da aiki a hukumar kula da harkokin jami’o’i ta kasa har zuwa 2026, ba zai iya cin ma wannan dogon buri ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel