Gwamnan Jihar Zamfara Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Tallafi

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Tallafi

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya ƙaddamar da rabon kayan tallafin abinci ga al'ummar jihar
  • Gwamnan ya ƙaddamar da fara rabon kayan tallafin ne domin rage raɗaɗin cirw tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi
  • Gwamna Dauda ya buƙaci kwamitin rabon kayan tallafin da su yi aiki tsakaninsu da Allah, sannan ya sha alwashin hukunta duk wanda ya karkatar da tallafin

Jiihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Talata ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi a jihar.

Gwamnan ya nanata cewa rabon kayan tallafin abincin na dukkanin al'ummar jihar ne ba tare da la'akari daga jam'iyyun da suka fito ba.

Gwamna Dauda ya kaddamar da rabon tallafi
Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da rabon tallafi Hoto: Sulaiman Bala Idris
Asali: Facebook

A wajen ƙaddamar da rabon kayan tallafin, Dauda ya yi kira ga kwamitin da aka ɗora alhakin rabon kayan a kansu, da su tabbatar sun yi gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Tsadar Fetur: Yadda Abba Gida Gida Ya Yi Rabon Kayan Tallafi ga Mata da Manoma

Mataimakin gwamnan jihar Mallam Mani Mallam Mummuni shi ne zai jagoranci ƙwamitin rabon kayan tallafin na abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na Facebook.

A cikin sanarwar, gwamna Dauda ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin matakan farko don ragewa mutane raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Yadda rabon tallafin zai kasance

Sanarwar na cewa:

"Gwamnati za ta raba buhunan shinkafa dubu 11, 877 da kuma buhunan shinkafa 2, 834, wanda za ta raba su ga ƙananan hukumomi shida."
“Kaso na biyu na tallafin za a yi shi a ƙananan hukumomi takwas wanda za a fara lokacin da gwamnati ta karɓi ragowar tallafin daga hannun gwamnatin tarayya."
“A cikin tallafin za a ba kowacce ƙaramar hukuma buhunan shinkafa 2,000 da buhanan takin zamani domin amfanin gona."

Kara karanta wannan

Ana Cikin Yajin Aiki, Gwamnan Arewa Ya Bai Wa Ƙungiyar NLC Manyan Tireloli Makare da Buhunan Shinkafa

Sulaiman a cikin sanarwar ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta fara ba ɗalibai ƴan asalin jihar tallafin karatu.

Ana Cin Dusa Saboda Yunwa a Zamfara

A wani labarin na daban, al'umma a wasu ƙauyukan jihar Zamfara na cikin mawuyacin hali saboda rashin tsaron da su ke fama da shi.

Rashin tsaron ya yi ƙamari wanda har ya kai ga wasu na cin dusa domin su tsira da rayukansu, yayin da wasu daga cikinsu suka koma mabararan ƙarfi da yaji domin samun abin da za su ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel