Rashin Tsaro: Yadda Al’umma Ke Cin Dusa Don Rayuwa a Jihar Zamfara

Rashin Tsaro: Yadda Al’umma Ke Cin Dusa Don Rayuwa a Jihar Zamfara

  • Al'ummar wasu kauyukan jihar Zamfara na cikin mawuyacin hali saboda hare-hare da ayyukan yan bindiga a yankin
  • Mazauna kauyuka kamar su Magami, Yar Tasha da sauransu sun koma cin dusa da yawon barace-barace saboda tsananin yunwa
  • Babban makasudin shiga wannan hali da suka yi saboda rashin samun yancin fita gonakinsu balle har su yi noman da za su iya rike kansu

Jihar Zamfara - Yayin da jihar ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro da hare-haren yan bindiga, al'ummar wasu yankunan Zamfara sun bayyana cewa dusa suke ci a yanzu domin rayuwa saboda tsananin yunwa.

Hakazalika, sun ce wasu daga cikinsu sun koma harkar barace-barace saboda samun na sawa a bakin salati.

Al'ummar wasu kauyukan Zamfara na cikin matsin rayuwa
Rashin Tsaro: Yadda Al’umma Ke Cin Dusa Don Rayuwa a Jihar Zamfara Hoto: @Kdankasa
Asali: Facebook

Rahotanni sun dai nuna cewa yankunan Wanke, Magami, Yar Tasha, Dan Sadau, Dan Kurmi da dai sauran yankunan jihar Zamfara na fama da matsalar rashin tsaro wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa

Sashin Hausa na BBC ta rahoto cewa mafi akasarin mazauna wadannan kauyuka suna cikin halin wayyo Allah sakamakon tsananin azabar da suke sha da hana su rawar gaban hantsi da yan bindiga ke yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A hirarsu da BBC, wani magidanci a jihar ya bayyana cewa mutum bai isa ya tashi daga garin Gusau ya ce zai je Magami ba, ba tare da jami'an tsaro sun yi masa rakiya ba.

A cewarsa, idan mutum ya taso daga garin Gusau, sai ya yada zango a wani gari da ke kan hanya sannan ya yi kwanaki amma tsakanin Magani da Janguma kilomita 25 kawai, amma rashin tsaro ya sa duk wanda ya bi wajen sai ya yi bara.

Yadda matsalar tsaro ta nakasa harkokin noma a Zamfara

An tattaro cewa rashin fita noma yana daya daga cikin dalilan da suka sake nakasa al'ummar wadannan kauyuka domin basu da yancin zuwa gonakinsu balle su yi noma.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Miyagun 'Yan Fashi Sun Kai Kazamin Hari Yankuna Uku a Babban Birnin Jihar PDP

Wasu manoma a yankin sun ce basu da ikon yin tafiyar kilomita guda daga garin Magami ba tare da an sake ko harbe mutum ba.

Wani manomi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa a halin da ake ciki, mutanensu da ke hannun yan bindiga sun kai 20, wasu kuma sun fita amma basu dawo da rai ba.

Ya ce mutane kan kwashe kwana biyu ba tare da sun sa abinci a bakinsu ba. Ana ta sakin mata saboda babu abun basu inda kananan yara suka koma barace-barace.

Yan bindiga sun fara amfani da dabarun 'yan ta'adda don yin barna, Sojoji

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara, ta sanar da rufe kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi biyar na jihar sakamakon matsalar tsaro.

Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Zamfara, Mannir Mu’azu Haidara ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng