Labarin wata mahaifiya da ta sanya 'yar ta kukan dadi

Labarin wata mahaifiya da ta sanya 'yar ta kukan dadi

Wata mahaifiya ta yiwa 'yar ta gagarumar kyauta har ta fashe da kuka saboda murna

Ita rayuwa daman ance komai ka shuka to shi kuwa za ka girba kuma kowa kaga ya samu wani abu to rabon shi ne tsaga.

Wata mahaifiya ta yiwa 'yar ta gagarumar kyauta inda har 'yar ta fashe da kuka saboda tsanin murna da jin dadi.

Labarin wata mahaifiya da ta sanya 'yar ta kukan dadi
Labarin wata mahaifiya da ta sanya 'yar ta kukan dadi

Ita wannan mahaifiya daman ta saba yiwa 'ya'yanta irin wannan kyautar ta bazata domin su ma su ji dadi kamar yadda su ka saka ta murna.

Mahaifiyar wannan yara daman ta sha yi musu nasiha a kan cewa lallai iyaka kokarinka da ka yi wajen faranta ma ta to ita ma za ta kwatanta da wata gagarumar kyauta don ita ma ta ga ran 'ya'yanta ya yi fari.

KU KARANTA: Rashin lafiyar Buhari: Wahalar ai ta kare inji Oyegun

A irin haka 'yar wannan mata ta baiwa 'yar ta kyuatar wayar sadarwa kirar iphone 7 saboda ta yi bajinta a jarabawar makaranta kuma ta fito da sakamako mai kyau wanda ko wane iyaye za su so 'ya'yan su da shi.

Daman dai babban buri wannan 'ya ta mallaki irin wannan wayar ta sadarwa kuma sai gashi mahaifiyarta ta cika ma ta wannan burin ba tsammani, wanda saboda tsanin murna ta rungume mahaifiyar ta hawaye.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel