Shehu Sani Ya Yabawa Abba Gida Gida Kan Matakin Hana Karin Kudin Makarantu A Jihar

Shehu Sani Ya Yabawa Abba Gida Gida Kan Matakin Hana Karin Kudin Makarantu A Jihar

  • Sanata Shehu Sani ya yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan matakin da ya dauka na hana karin kudin makarantu a jihar
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Gida Gida ya hana shirin karin kudin makaranta na makarantu masu zaman kansu na firamare da sakandare
  • Yayin da ya ke martani a kan hakan, Shehu Sani ya yabawa Abba Kabir tare da shawartar sauran gwamnoni da su kwaikwayi gwamnan

Jihar Kano – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yaba wa gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf kan matakin da ya dauka na makarantu masu zaman kansu.

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Talata 15 ga watan Agusta inda ya ce matakin na gwamnan abin a yaba ne.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Ke Jawo Mataimakan Gwamna Su Yi Fada da Gwamnoni a Jihohi – Ganduje

Shehu Sani ya yabawa Abba Gida Gida kan hana karin kudin makarantu
Shehu Sani Ya Yabawa Abba Gida Gida Kan Matakin Da Ya Dauka A Jihar. Hoto: @Kyusufabba, @ShehuSani.
Asali: Twitter

Me Sani ya ce kan Abba Gida Gida?

Ya ce matakin da ya dauka na hana makarantu masu zaman kansu da na gwamnati daga karin kudin makaranta ya yi jaruntaka, Legit ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kirayi sauran jihohi da su yi koyi da gwamnan saboda bai kamata iyaye su shiga matsala saboda Dala ta yi tsada ko kuma karin kudin fetur ba.

Ya ce:

“Matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na hana makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu karin kudin makaranta abin a yaba ne.
“Ya kamata sauran jihohi su yi koyi da hakan, Don Dala ta tashi ko kuma karin kudin fetur bai kamata ya shafi iyaye ba.”

Me mutane ke cewa kan Abba Gida Gida?

‘Yan Najeriya sun yi martani a kan abin da Shehu Sani ya wallafa.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

@MUgosman:

“Wannan shi ne adalci.”

@Shehumahmed:

“Gaskiya na yadda da kai a wannan layin, matakin gwamnatin Kano don hana karin kudin makaranta abin a yaba ne don samar da ilimi mai sauki ga kowa.”

@DayoOjo:

“Adalci kenan.”

Shehu Sani Ya Bayyana Dalilai 5 Da Ke Jawo Juyin Mulki A Afirka

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilai biyar da ke jawo juyin mulki a Nahiyar Afirka.

Sani ya bayyana haka ne yayin hira da kamfanin dillanin labaru ta NAN, inda ya ce magudin zabe da rashin tsaro na daga cikin dalilan.

Sauran dalilan sun hada da ruguza martabar dimokradiyya a Nahiyar Afirka musamman ta Yamma bayan hambarar da Mohamed Bazoum a Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel