Da Dumi- Dumi: Hukumar DSS Ta Gayyaci Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Kogi

Da Dumi- Dumi: Hukumar DSS Ta Gayyaci Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Kogi

  • Wasu ƴan jam'iyyun adawa sun rubuta ƙara ga hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) kan ɗan takarar gwamnan APC na jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo
  • Hukumar DSS ta gayyaci Ododo domin amsa tambayoyi bisa zarge-zargen dake cikin ƙarar da ƴan adawar suka shigar
  • Ɗan takarar na jam'iyyar APC ya amsa gayyatar ta hukumar DSS a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli, inda aka kwashe sa'o'i ana yi masa tambayoyi

Jihar Kogi - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta gayyaci ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, domin amsa tambayoyi bayan wasu ƴan jam'iyyar adawa sun shigar da ƙorafi a kansa.

Kwamishinan watsa labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, shi ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, @KingsleyFanwo, a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya 'Yan Bindiga Suka Kwamushe Ni, Babban Boka Ya Yi Bayani Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci

DSS ta gayyaci dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Kogi
Ahmed Usman Ododo ya samu gayyata daga hukumar DSS Hoto: @KingsleyFanwo
Asali: Twitter

Fanwo ya bayyana cewa ɗan takarar gwamnan ya amsa gayyatar da DSS ta yi masa a yau Asabar.

Fanwo ya bayyana cewa Ododo ya amsa gayyatar da hukumar DSS ta yi masa a matsayinsa na ɗan ƙasa nagari mai son jan ragamar jihar Kogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa ɗan takarar na jam'iyyar APC ya sha tambayoyi na tsawon sa'o'i masu yawa a hannun jami'an hukumar DSS.

A kalamansa:

"Zarge-zargen dake a cikin ƙarar soki burutsu ne kawai marasa tushe ballantana makama. Amma abu ne mai kyau da ɗan takarar gwamnan na APC ya mutunta hukuma mai girma kamar ta DSS."
"Alh. Ododo ya sha tambayoyi a hannun tawagar jami'an hukumar DSS na sa'o'i masu yawa, inda ya basu gamsassun amsoshi."

Kwamishinan ya yaba wa jami'an DSS

Fanwo ya bayyana cewa sun yaba da ƙoƙarin da jami'an hukumar DSS suka yi, inda ya tabbatar musu da cewa, za su basu dukkanin haɗin kan da su ke buƙata.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Yaransa 4 da Suka Addabi Mutane a Jihohin Arewa 2

Ya kuma kwantar da hankalin magoya bayan ɗan takarar gwamnan cewa tuni har ya bar ofishin hukumar ya ci gaba da harkokin gabansa.

Ododo Ya Zama Dan Takarar Gwamnan APC a Kogi

A baya rahoto ya zo cewa, Ahmed Usman Ododo ya zama ɗan takarar gwamnan APC a jihar Kogi, bayan ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.

Ahmed Usman Ododo wanda gwamna Yahaya Bello yake marawa baya, ya samu nasarar ne bayan ya doke sauran abokanan takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel