Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kulle Makarantu 5 Bayan Bullar Cutar Mashako

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kulle Makarantu 5 Bayan Bullar Cutar Mashako

  • Cutar Mashaƙo ta ɓulla a ƙaramar hukumar Jama'are ta jihar Bauchi inda ta halaka ɗalibai guda biyu
  • Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kulle makarantun da lamarin ya shafa domin daƙile ci gaba da yaɗuwar cutar
  • Gwamnatin ta kuma sanar da cewa duk makarantar da aka samu ɓullar cutar za a kulle ta nan take ba tare da ɓat lokaci ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar ɗalibai guda biyu a ƙaramar hukumar Jama'are a jihar a dalilin zargin ɓarkewar cutar Mashaƙo.

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi (BSPHCDA), Dr Rilwanu Mohammed, shi ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Laraba a Bauchi, rahoton Leadership ya tabbatar.

An kulle makarantu a Bauchi saboda Mashako
Cutar ta halaka dalibai guda biyu Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Dr Rilwanu ya bayyana cewa daga cikin samfurin ɗalibai 58 da aka ɗauka, biyu daga ciki sun rasu a sakamakon cutar mashaƙo, yayin da ake ci gaba da gudanar da gwaji akan sauran.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Sallami Sule Lamido Daga Zargin Karkatar Da Miliyan 712 Da Ake Yi Ma Sa, Ta Fadi Dalilin Hakan

Ya bayyana cewa hukumar a shirya take domin ganin ta hana yaɗuwar cutar, inda ya ƙara da cewa za a yi allurar rigakafi domin hana yaɗuwar cutar, cewar rahoton Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu fara yi wa yaranmu rigakafin tun suna mako shida a duniya, kuma babban abin jindaɗin allurar kyauta za a riƙa yinta." A cewarsa.

Abinda gwamnatin jihar take yi domin daƙile yaɗuwar cutar

Dr. Mohammed ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kulle dukkanin makarantun da abun ya shafa a ƙaramar hukumar domin yin takatsantsan da yaɗuwar cutar

Shugaban hukumar ta BSPHCDA ya kuma yi nuni da cewa duk wata makaranta a jihar inda aka tabbatar da ɓullar cutar Mashaƙo za a kulle ta.

Cutar Mashaƙo dai ta fara yaɗuwa a wasu jihohi na Arewacin Najeriya, wacce alamominta sun haɗa da alamomin cutar sun hada da zazzabi da kaikayin maƙoshi da kan fara cikin kwanaki biyu zuwa biyar na haduwa da kwayoyin cutar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Sanya Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Kama Ganduje Bisa Bidiyon Dala

Mashako Ta Halaka Yara 30 a Yobe

A wani labarin kuma, cutar Mashaƙo ta yi sanadiyyar rasuwar yara guda 30 a jihar Yoɓe dake yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Cutar ta ɓulla ne a wasu sassan jihar inda a dalilin hakan aka killace mutum 42 a asibitin ƙwararru dake Potiskum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel