Cutar Mashako Ta Halaka Yara 30 a Jihar Yobe, Ta Kwantar Da Wasu 42 a Asibiti

Cutar Mashako Ta Halaka Yara 30 a Jihar Yobe, Ta Kwantar Da Wasu 42 a Asibiti

  • Wata sabuwar cuta ta mashako da ta bulla a jihar Yobe, ta yi sanadiyyar mutuwar yara akalla 30
  • Cutar ta mashako ta kuma yi sanadiyyar kwantar da yara sama da 40 a sashen killace mutane na asibitin kwararru da ke Potiskum
  • Wani daga cikin iyayen yaran da ya zanta da manema labarai ya ce mafi yawan yara na mutuwa ne a gida gabanin kawo su asibiti

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Potiskum, Yobe - Wata sabuwar cuta ta mashako da ta bulla a jihar Yobe, ta yi sanadin mutuwar yara 30, tare da aikawa da wasu 42 da yanzu haka aka killace a asibitin kwararru da ke Potiskum.

Tandari, Titin Misau, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Igwanda da rukunin gidaje na Texaco ne yankin da annobar ta fi shafa kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Motar da ta dauko masu zuwa 'party' ta yi karo da motar yashi, mutum 20 sun mutu

Cutar mashako ta kashe akalla yara 30 a jihar Yobe
Sabuwar cuta ta mashako ta kashe yar akalla 30 a jihar Yobe. Hoto: NFID
Asali: UGC

Ana fuskantar karancin magungunan da za a kula da wadanda suka kamu da cutar

Wata majiya a cibiyar killace mutane ta asibitin kwararru da ke Potiskum, ta bayyana cewa suna fuskantar karancin magungunan da za su shawo kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce kawo yanzu an kawo kimanin mutane 46, inda aka samu mutuwar mutane biyar daga cikinsu.

An bayyana cewa akalla yara 20 ne suka mutu a gida, yayin da wasu karin hudu suka mutu a asibiti.

Yara da dama sun rasu a gida kafin a kawo su asibiti

Wani daga cikin iyayen yaran da lamarin ya rutsa da su da bayyana sunansa da Abdullahi Muhammad, ya ce yara da dama sun mutu a gida kafin a kawo su asibiti.

Muhammad ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki cikin gaggawa don ceto rayuwar ‘ya’yansu. A kalaman Muhammad:

Kara karanta wannan

'Ba Mu San Laifin Da Muka Aikata Ba', Wadanda Ake Zargin Yan Boko Haram Da Ke Tsare A Barikin Giwa

“Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin ceto rayukan ‘ya’yanmu. Alamomin da muka lura da su sun hada da zazzabi, tari, raunin jiki da sauransu.”

Da aka tuntubi jami’in rigakafi na shiyyar Potiskum Mallam Buba, ya musanta alkaluman wadanda aka ce sun mutu, sai dai ya tabbatar da cewa akwai akalla yara 42 da ke kwance a asibiti.

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka (CDC), sun bayyana a shafinsu na Intanet cewa, alamomin cutar sun hada da zazzabi da kaikayin makoshi da kan fara cikin kwanaki biyu zuwa biyar na haduwa da kwayoyin cutar.

Legit.ng ta tuntubi Dakta Ibrahim Usman Dabai, na asibitin koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Katsina domin ƙarin haske akan wannan sabuwar cuta ta mashako.

Ya ce wata ƙwayar halitta da ake kira da Corynebacterium diphtheriae ce ke haifar da wannan nau'in cutar ta mashako.

Ya bayyana cewa cutar ba sabuwar aba ba ce, illa iyaka an yi nasarar daƙile ta ne a can baya kafin sake ɓullarta a yanzu.

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

Ya ƙara da cewa alamominta sun yi kama da alamomin mura, sai dai bayan kwanaki kaɗan, za ta fara nuna ainihin alamominta da suka haɗa da wahala wajen yin numfashi, zazzaɓi, da kuma ƙaiƙaiyin magogwaro.

Dakta Ibrahim ya kuma bayyana cewa, ana iya kamuwa da cutar ta hanyar cuɗanya da waɗanda ke ɗauke da ita, kamar ta hanyar sumbata ko ta hanyar haɗa jiki.

Masu cutar ma a cewarsa, za su iya yaɗawa mutane ita ta hanyar yin tari ba tare da rufe bakunansu ko hancinsu ba.

Daga cikin hanyoyin da za a iya kare kai daga kamuwa da cutar kamar yadda Dakta Ibrahim ya yi bayani, akwai yin rigakafin cutar na musamman ga yara ƙanana.

Haka nan ya ba da shawarar garzayawa zuwa asibiti da zarar an lura da alamomin cutar don ɗaukar matakan gaggawa.

Gwamnatin Tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya kan cin ganda

Legit.ng a wani rahoto ta kawo muku gargadin da Gwamnatin Tarayya ta yi na cewa ‘yan Najeriya su kiyayi cin ganda ko naman da aka burara.

Kara karanta wannan

Hajiya Halimatu Attah: Fasinjar Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Mafi Tsufa Da Aka Yi Garkuwa Da Ita Ta Rasu

Gargadin dai na zuwa ne saboda bullar wata sabuwar cuta mai suna ‘Anthrax’ a wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel