Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Zargin Karkatar Da Miliyan 712 Da Ake Yi Wa Sule Lamido

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Zargin Karkatar Da Miliyan 712 Da Ake Yi Wa Sule Lamido

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta sallami tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido daga zargin da ake masa
  • Kotun ta yi hukuncin ne bisa rashin cika ƙai'ida da kuma rashin gamsassun hujjoji daga ɓarin masu shigar da ƙara
  • Kotun ta ce a jihar Jigawa ya fi dacewa a shigar da ƙarar saboda a can ne aka aikata laifin da ake tuhumarsa da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kotun daukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta sallami Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, tare da ‘ya’yansa maza biyu bisa zargin karkatar da kuɗaɗe har naira miliyan 712.

A hukuncin da ta yanke a ranar Talata, kotun ta amince da buƙatar waɗanda ake ƙara na watsi da shari'ar bisa rashin isassun hujjoji kamar yadda rahoton The Cable ya nuna.

Kotun ɗaukaka ƙara ta sallami Sule Lamido
Kotun ɗaukaka ƙara ta sallami Sule Lamido daga zargin badaƙalar naira miliyan 712 da ake tuhumarsa. Hoto: Abba Sa'adu Hadejia
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Kotu Ta Sanya Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Kama Ganduje Bisa Bidiyon Dala

Dalilin kai Sule Lamido da 'ya'yansa kotu

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ce ta shigar da Sule Lamido kotu tare da ‘ya’yansa biyu, Aminu da Mustapha a shekarar 2015.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar ta gabatar da tuhume-tuhume guda 37 dake da alaƙa da badaƙalar kuɗaɗe kan Lamido da 'ya'yan nasa a gaban kotu.

Haka nan daga cikin waɗanda hukumar ta EFCC ta maka a gaban ƙuliya, akwai abokin kasuwancin Lamido mai suna Aminu Abubakar.

EFCC ta haɗa da wasu kamfanoni guda huɗu wato Bamaina Company Nigeria Limited, Bamaina Aluminium Limited, Speeds International Limited da kuma Batholomew Darlington Agoha, waɗanda ke da alaƙa da Sule Lamido cikin shari'ar.

Sule ya nemi a yi watsi da shari'ar bisa rashin hujjoji

A shekarar 2022, Sule Lamido ya nemi kotu ta yi watsi da shari'ar saboda rashin gamsassun hujjoji, sai dai buƙatarsa ba ta samu karɓuwa ba a lokacin, wanda hakan ya sanya shi daukaka ƙara.

Kara karanta wannan

Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana

Da yake yanke hukunci, mai shari'a Adamu Waziri na kotun ɗaukaka ƙara ya bayyana cewa bai ma kamata kotun baya ta saurari shari'ar ba tunda ba a inda take aka yi laifin da ake zargin ba.

Ya ce a jihar Jigawa ne ya kamata a ce an shigar da ƙarar tunda a can ne aka aikata laifin da ake tuhumarsa Lamidon da shi kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Daga ƙarshe mai shari'a Adamu Waziri ya sallami Sule Lamido da 'ya'yan nasa.

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci dangane da batun kama Ganduje kan bidiyon dala

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan batun kama Ganduje dangane da bidiyon dala.

Kotun ta tsayar da ranar 22 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan neman dakatar da hukumar PCACC daga kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel