Hayakin Janareto Ya Yi Sanadin Mutuwar Ma'aurata Da 'Yayansu 2 a Jihar Anambra

Hayakin Janareto Ya Yi Sanadin Mutuwar Ma'aurata Da 'Yayansu 2 a Jihar Anambra

  • Hayaƙin janareto ya yi sanadin mutuwar mutane shida a Onitsha da ke jihar Anambra
  • Mamatan sun haɗa da ma'aurata, 'ya'yansu biyu, surukarsu da mai taya su aiki
  • An bayyana cewa marigayan sun tare ne a sabon gidan da mijin ya bai wa matarsa matsayin kyauta na murnar haihuwa da ta yi

Anambra - Jami'an 'yan sandan jihar Anambra sun tabbatar da mutuwar ma'aurata, 'ya'yansu biyu da ƙarin wasu mutanen biyu a yankin Nkwele Ezunaka da ke garin Onitsha.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ma'auratan, 'ya'yansu biyu, surukarsu da kuma mai taya su aiki sun rasu ne ranar Laraba, sakamakon shaƙar hayaƙin janareto da suka yi.

Hayaƙin janareto ya janyo mutuwar mutane 6 a Anambra
Ma'aurata, 'ya'yansu biyu da wasu mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon hayaƙin janareto. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Sun rasu suna murnar komawa sabon gida

Rahoton ya tattaro cewa ma'auratan sun tare ne a sabon gidansu wanda mijin ya yi wa matarsa kyauta ta murnar sabuwar haihuwa da ta yi.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An bayyana cewa, a daren farko da suka shafe a sabon gidan ne wannan mummunan al'amarin ya faru, inda jaririn ne kawai daga cikinsu ya rayu.

An samu cewa wani daga cikin abokan mai gidan ne da bai samu damar zuwa murnar a daren ba ya zo gidan da safe, inda ya tarar da ƙofofin gidan a rufe, a yayin da janareton kuma yake a kunne.

Maƙwabtansu sun kawo ɗauki bayan sanin halin da ake ciki

Mutumin ya yi ƙoƙarin sanar da maƙwabtan mamatan, waɗanda da taimakonsu ne aka yi nasarar ɓalle ƙofar, inda aka tarar da su kwance, wasu ba bu rai wasu kuma sun jigata.

Mutumin ya ce an yi ƙoƙarin kai matar da kuma ɗiyarta guda ɗaya asibiti, inda daga bisani aka tabbatar da cewa suma sun rasu kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tallafin Man Fetur: Taliya, Gari Da Rukunin Abubuwa 5 Da Zaka Iya Saya Da Naira 8,000

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ta Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwa lamarin, sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba su kammala bincike ba kan ainihin abinda ya yi sanadin mutuwar mutanen.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ta Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwa lamarin, sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba su kammala bincike ba kan ainihin abinda ya yi sanadin mutuwar mutanen.

Mutane shida sun mutu bayan shan barasa a jihar Ogun

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan wasu abokanai shida da suka rasa rayukansu sakamakon wata barasa da suka kwankwaɗa a jihar Ogun.

An bayyana cewa wanda ya kawo musu barasar, wanda abokinsu ne, bai mutu ba kuma yanzu haka ya ranta a na kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel