Innalillahi: Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Kwamishiya a Jihar Kano Rasuwa

Innalillahi: Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Kwamishiya a Jihar Kano Rasuwa

  • Tsohuwar kwamishiyar ma'aikatar harkokin mata da ma'aikatar kasafinda tsare-tsare ta jihar Kano ta riga mu gidan gaskiya
  • Barr. Zubaida Damakka Abubakar ta rasu ne bayan ƴar gajeurwar jinya a wani asibiti a birnin tarayya Abuja ranar Asabar, 22.ga watan Yuli
  • Za a gudanar da jana'izar marigayiyar wacce ita ce manajar kamfanin madara na L&Z ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli a birnin Kano

Jihar Kano - Allah ya yiwa tsohuwar kwamishiniya a ma'aikatar harkokin mata da ma'aikatar kasafi da tsare-tsare ta jihar Kano, Barr. Zubaida Damakka Abubakar, rasuwa.

Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, a wani asibiti dake a birnin tarayya Abuja.

Tsohuwar kwamishiniya a Kano ta rasu
Barr. Zubaida ta rasu bayan yar gajeruwar jinya Hoto: Barr. Zubaida Damakka Abubakar
Asali: Facebook

Za a gudanar da jana'izar marigayiyar a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli, a gidansu dake a Unguwar Gwammaja cikin birnin Kano, da ƙarfe 9:00 na safe.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kano: Abba Gida Gida Ya Rufe Shari’a Da Baffa Bichi a Matsayin Shaida Shi Kadai

An bayyana labarin rasuwar marigayiyar ne a shafinta na Facebook, cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar na cewa:

"Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun. Allah ya yi wa Barr. Zubaida Damakka Abubakar Rasuwa yau a garin Abuja bayan gajeriyar rashin Lafiya."
"Za ayi Jana'izarta gobe insha Allah a gidansu dake bayan Sakandire ta Gwammaja 2 Layin karo da goma da karfe 9 na safe. Muna fatan Allah ya jikanta da rahma yasa aljanna makomarta, ya amfani bayanta."

Marigayiya Barr. Zubaida ta taɓa riƙe kujerar kwamishina a ma’aikatar harkokin mata da ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta Jihar Kano, a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Har zuwa lokacin rasuwarta, marigayiyar ita ce manajar shahararren kamfanin madarar nan na L&Z.

Marigayiyar tana daga cikin kwamishinonin da tsohon gwamna Ganduje ya sauke daga muƙamansu a shekarar 2017.

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Mallaki Sabon Digiri a Jami’ar Oxford, Bidiyo Ya Bayyana

Babban Limamin Juma'a a Fagge Ya Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa babban limamin masallavin Juma'a na Fagge dake a jihar Kano rasuwa.

Sheikh Nasir Muhammad Nasir wanda aka fi sani da limamin waje, ya koma ga mahaliccinsa ne yana da shekara 87 a duniya. Marigayin ya taɓa riƙe sarautar wazirin Sarkin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel