Babban Malamin Addini A Najeriya Ya Magantu Kan Zargin Cewa Yana Aiki Da Kwankwamai

Babban Malamin Addini A Najeriya Ya Magantu Kan Zargin Cewa Yana Aiki Da Kwankwamai

  • Fasto Enoch Adeboye, babban mai kula da majami'ar RCCG ya yi karin haske a kan zargin amfani da kwankwamai
  • Ya bayyana haka yayin hudubarsa ta jiya lahadi 16 ga watan Yuli, inda ya ce maganar ba ta da tushe bare makama.
  • Ya ce ya ji wani ya na zargin shi da amfani da aljanu, amma abinda kawai zai iya yi masa addu'a don neman tsira

FCT, Abuja - Babban mai kula da majami'ar Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye ya karyata cewa yana amfani da kwankwamai a majami'ar.

A yayin hudubarsa ta jiya lahadi 16 ga watan Yuli, Adeboye ya ce wannan zargi ne wanda ba shi da tushe bare makama, Daily Trust ta tattaro.

Malamin Addini Ya Magantu Kan Zargin Cewa Yana Aiki Da Kwankwamai’
Fasto Enoch Adeboye Ya Musanta Zargin Cewa Yana Aiki Da Kwankwamai A Majami'arsa. Hoto: Legit.ng.
Asali: Twitter

Malamin addinin ya ce zargin aiki da kwankwamai ba gaskiya ba ne

Kara karanta wannan

Gardamar Shinkafa Ta Jawo Yaron Gida ya Kashe Malami da Tabarya Cikin Dare

Ya ce wannan zargi ya fito ne daga bakin wani mutum inda madadin mai da martani ga mutumin, ya yanke shawarar yi masa addu'a, cewar Tori News.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani faifan bidiyo da ke yawo, an gano Fasto Adebayo ya na cewa:

"Na ji wani na cewa Fasto Adeboye yana aiki da kwankwamai da yake samun karfi daga gare su a sansanin majami'ar Redemption.
"Wasu mutane suna cewa ba zan mai da martani a kan hakan ba? Sai na ce a'a ya na bukatar addu'a ne saboda ya na aikata babban zunubi wurin hada karfin ikon ubangiji da na aljanu.
"Haka suke fada akan Annabi Isa suna cewa ya na amfani da aljanu."

Ya ce wanda ya yi wannan sabo addu'a ya ke bukata

Adeboye ya kara da cewa:

"Idan ka ji wani ya fadi irin haka, to addu'a ya kamata a yi masa, saboda Annabi Isa ma ya na da inda ba a tsallakewa.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Kasa Adamu Abdullahi Ya Yi Murabus Ne? Ga Abin Da Muka Sani

"Ya ce idan ka yi sabo ga Allah uba, zai ya yafe maka, haka sabo ga Allah 'da', amma idan ka yi a kan ruhu mai tsarki to ka gama yawo."

Cocin RCCG ta yi magana akan ganawar sirri da aka yi da Tinubu

A wani labarin, majami'ar RCCG ta yi bayanin ganawar da babban mai kula da majami'ar, Fasto Enoch Adeboye ya yi da dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu.

Adeboye ya ce ba kamar yadda ake yadawa ba, shi bai gana da Bola Tinubu a kan tikitin Musulmi da Musulmi ba.

Wata jarida ta kasa ta ce Bola Tinubu ya gana da Fasto Enoch Adeboye akan takarar sa a karshen makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel