Gwamnatin Katsina Ta Kwantar da Hankalin Malaman S-Power, Ta Fadi Mataki Na Gaba

Gwamnatin Katsina Ta Kwantar da Hankalin Malaman S-Power, Ta Fadi Mataki Na Gaba

  • Gwamnatin Dikko Radɗa ta yi bayani domin yaye tsoron da ya mamaye zuƙatan malaman makaranta na shirin S-Power a Katsina
  • Sakataren gwamnatin jihar, Ahmad Dangiwa, ya ce babu wani abinda tsoro ko karaya game da jarabawar gwajin da za'a shirya musu
  • A watan Mayu wa'adin aikin wucin gadin malaman ya ƙare amma gwamna ya ce zai basu aikin dindindin bayan an tantance su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Malam Dikko Umaru Radɗa ta yi ƙarin haske domin kwantar da hankulan malaman makaranta 7,000 na tsarin S-Power.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin Dikko ta tabbatar wa malaman, waɗan da tun asali aka ɗauka a matsayin aikin wucin gadi cewa zata duba yiwuwar ɗaukar su aiki ko wani abun daban.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda.
Gwamnatin Katsina Ta Kwantar da Hankalin Malaman S-Power, Ta Fadi Mataki Na Gaba Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin Katsina (SSG), Arc. Ahmed Musa Dangiwa, shi ne ya bada wannan tabbaci yayin da ya karɓi bakuncin Malaman S-Power a ofishinsa ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Yi Fatali Da Batun Tallafin Karatu a Jiharsa, Ya Bayar Da Dalilai

Malaman S-Power na Katsina a taƙaice

Tsohuwar gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ce ta ɗauki malamai 7,000 a shirin da ta kirkiro da shi mai suna S-Power mai kama da N-Power.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ɗaukarsu aikin wucin gadi, tsohuwar gwamnati ta tura su makarantun Firamare da Sakandire da ke faɗin kananan hukumomi 34 na jihar.

Mataki 2 da zamu ɗauka kafin ɗaukarsu aiki - Gwamna Raɗda

A halin yanzu, bayan ƙarewar aikin wucin gadin malaman a karshen watan Mayu, Malam Dikko Raɗɗa ya yi alkawarin ɗaukarsu aikin dindindin amma bisa sharaɗi.

Bisa la'kari da gudummuwar da suka bayar, gwamna Raɗɗa ya yi alkawarin ɗaukarsu aiki amma bayan an tantance su kuma sun zauna jarabawar gwaji.

Wannam batu na cewa sai an musu gwaji kuma an tantance su ya jefa tsoro a zuƙatan malaman makarantar na tsarin S-Power, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Nada Tsohon Ministan Shugaba Goodluck Jonathan a Matsayin Sabon SSG

Kar ku ji tsoron gwajin da za'a muku - Gwamnatin Katsina

Da yake jawabi ga ƙungiyoyin malaman S-Power guda biyu, na Sakandire da Firamare, Sakataren gwamnatin ya faɗa musu karsu ji tsoro ko su karaya da jarabawar gwajin da za'a musu.

Ya ƙara da cewa za'a gwada su ne domin tabbatar da cewa waɗan da suka cancanta ne kaɗai za'a damƙa wa amanar ilimin ƙananan yaran jihar Katsina.

Mun tuntubi wani malamin sakandire a tsarin S-Power, Saifullahi Lawal, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa an fara tantance su kafin kuma su yi jarabawa.

Ya ce suna fatan a yi adalci a waɗan nan matakai da sabuwar gwamnati ta zo da su wajen ɗaukarsu aikin dindindin. A cewarsa suna tsoron yan siyasa su shiga ciki.

Ya ce:

"Eh jiya (Talata) wakilanmu sun je gidan gwamnati kuma yau (Laraba) muka je Funtua aka tantance mu, har yanzu ba a sanya ranar jarabawa ba amma muna sa ran a wata mai zuwa."

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata da Dukkan Hadiman Da Magabacinsa Ya Naɗa Nan Take

"A zahirin gaskiya wannan gwamnati ta zo da niyyar aiki to amma mu 'yan S-power an barmu a duhu, ba'a ce mana aikinmu ya ƙare ba kuma ba a biya mu alawus ɗin watan Yuni ba har yanzu."

Gwamnan Neja Ya Kori Dukkan Hadiman da Tsohon Gwamna Ya Nada

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Neja, Umar Bago, ya kori hadiman da magabacinsa ya naɗa a muƙamai daban-daban gabanin ranar 29 ga watan Mayu.

Bugu da ƙari, Gwamna Bago ya rushe baki ɗaya majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnati wanda magabacin ya naɗa a lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel