Allah Ya Yi Wa Shugaban Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Shugaban Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano Rasuwa

  • Al’ummar karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano sun shiga jimami na wani babban rashi da suka yi
  • Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Bebeji, Alhaji Sani Kanti Ranka, rasuwa a ranar Juma'a
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika ta’aziyyarsa tare da yi wa marigayin addu’a samun rahmar Ubangiji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano, Alhaji Sani Kanti Ranka, rasuwa a daren ranar Juma'a, 8 ga watan Yuli.

Marigayi Sani ya rasu ne bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya kuma an binne shi bisa koyarwar addinin Musulunci a ranar Asabar, 9 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Shugaban karamar hukumar Bebeji. Sani Kanti Ranka ya rasu
Allah Ya Yi Wa Shugaban Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano Rasuwa Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Marigayi Sani mutum ne mai son zaman lafiya, Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin mutuwar

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa a kan mutuwar shugaban karamar hukumar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mara hayaniya mai son zaman lafiya da tarin sani a harkar siyasa da bautawa mutane.

Ya kuma yi masa addu'an samun Rahamar Allah da aljannah madaukakiya.

Ya rubuta a shafinsa:

"Cike da bakin ciki na samu labarin mutuwar Alhaji Sani Kanti Ranka, shugaban karamar hukumar Bebeji.
"Ya kasance mutum mai son zaman lafiya da tarin sani a siyasa da yi wa mutane hidima.
"Allah madaukakin sarki ya yafe masa kura-kuransa sannan ya saka masa da kyawawan ayyukansa da aljannatul Firdau. - AKY."

Jama'a sun yi wa mamacin addu'a tare da mika ta'aziyyarsu

@yakubwudil ya yi martani:

Kara karanta wannan

Innalillahi: Sarkin Musulmi da wani fitaccen sarki a Arewa sun yi rashin surukinsu

"Allah ya rahama masa, yasa aljanna makoma."

@ABBAMAIADDA ya ce:

"Allah ya jiƙansa da rahama."

@Aliyusanizaki ya ce:

"Allah ya jikansa."

@bin_saless ya ce:

"Allah Ya gafarta masa Yasa ya huta."

@shaba_isah ya rubuta:

"Allahunma agfirlahum war hamhum wa afu anhum. Aameen."

@mijinyawa77 ya ce:

"Allah ya jikansa ya Kwanta makwanci."

Allah ya yi wa Hajiya Halimatu Attah rasuwa

A wani labarin kuma, mun ji cewa matar nan da ta fi kowa tsufa cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 63 da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris din 2022, ta rasu tana da shekaru 85 a duniya.

Hajiya Halimatu Attah ta rasu a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli da misalin karfe 6:20 na yamma a Kaduna kamar yadda wani danginta ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel