Allah Ya Yi Wa Surukin Sarkin Bichi da Sarkin Musulmi Rasuwa a Birnin Landan Ta Burtaniya

Allah Ya Yi Wa Surukin Sarkin Bichi da Sarkin Musulmi Rasuwa a Birnin Landan Ta Burtaniya

  • Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi, da Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi a jihar Kano, sun shiga jimami
  • Aminu Haliru, jami’in hulda da jama’a na Majalisar Sarkin Musulmi, ya tabbatar da mutuwar surukin Sarkin Musulmi da Sarkin Bichi a ranar Asabar, 8 ga Yuli, 2023
  • A cewar Haliru, Sarkin Musulmi da Sarkin Bichi duk suna auren ‘ya’yan marigayin, dattijon kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar da Sarkin Bichi na jihar Kano, Alhaji Nasir Ado Bayero, sun yi rashin dan uwansu Abubakar Imam Galadanchi.

Marigayin ya rasu ne a birnin Landan bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda majiya ta bayyana.

Jami’in hulda da jama’a na Majalisar Sarkin Musulmi, Aminu Haliru ne ya tabbatar wa wakilin jaridar Daily Trust rasuwar a ranar Asabar 8 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC

Sarkin Musulmi da na Bichi sun yi rashin suruki
Sarkin Muslmi da Sarkin Bichi | Hoto: NTA Network News, Daily Trust
Asali: Facebook

A cewarsa, an aura wa Sarkin Musulmi da Sarkin Bichi ‘ya’yan marigayin a shekarun baya da suka shude.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya zuwa yanzu, rahotanni basu bayyana adadin 'ya'ya, jikoki da kuma gwagwarmaya ta rayuwar marigayin ba.

Fatan Allah ya jikansa ya kuma gafarta masa, wannen ne addu'ar da al'ummar Musulmin da suka ji labarin mutuwar ke yiwa marigayin.

Basarake ya kife a cikin fada, ya rasu a hanyar tafiya Masallaci

Wani Basarake a kasar Yaba a karamar Hukumar Abaji a babban birnin tarayya na Abuja, Alhaji Abdullahi Adamu ya rasu.

Mai martaba Abdullahi Adamu ya rasu ne a daren Juma’ar nan, labarin cikawarsa ta zo a jaridar nan ta Daily Trust a yammacin Alhamis. Wani ‘danuwan Sarkin, Shuaibu Abdullahi ya tabbatarwa manema labarai cewa an rasa Basaraken.

Malam Shuaibu Abdullahi ya ce Etsun Yaba ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake hanyar zuwa sallar Magriba a cikin fadarsa a jiya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sojoji Sun Bindige Yan Ta'addan Boko Haram, ISWAP Yayin Da Suke Tsallakowa Najeriya Daga Kamaru, Bayanai Sun Fito

Basarake a Jigawa ya kwanta dama a hadarin mota tare da yaransa 3

A bangare guda, Alhaji Muhammad Suleiman, dan Amar na Dutse kuma hakimin Basirka a jihar Jigawa ya riga .

Mai sarautar gargajiyar ya rasu tare da yayansa uku bayan motar da suke ciki ta yi hadari a kan hanyar Basirka Gwaram lokacin da suke hanyarsu ta zuwa garin Gwaram.

Matarsa da sauran yayansu biyu sun tsira daga hadarin, a cewar Sarkin Yakin Dutse, Abubakar Dutse, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel