Mahaifiyar Dan Majalisar Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ta Rasu

Mahaifiyar Dan Majalisar Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ta Rasu

  • Dan majalisar Tarayya a mazabar Irepo-Oorelope da ke jihar Oyo ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Alhaja Nusiratu Ajike
  • Dan majalisar, Prince Olaide Lateef Muhammad ya ce marigayiyar ta rasu ne da safiyar yau Juma’a 7 ga watan Yuli
  • Ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi jana’izarta koyarwar addinin Musulunci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo – Dan majalisa mai wakiltar mazabar Irepo-Oorelope a majalisar Tarayya a jihar Oyo, Prince Olaide Lateef Muhammad ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa Alhaja Nusiratu Ajike.

Prince Olaide, jigo a jam’iyyar APC daga jihar Oyo ya sanar da rasuwar marigayiyar ce a shafinsa na Facebook a yau Juma’a 7 ga watan Yuli.

Mahaifiyar Dan Majalisar Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ta Rasu
Marigayiya Alhaja Nusiratu Ajike. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

A sanarwar tasa, ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin wata katanga ga iyalansu gaba daya inda ya ce za su yi kewarta a wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Rigima Kan Gado Ta Kai Iyalin Tsohon Gwamna Kotu

Ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta rasu inda ya ce za su yi jimamin rashinta

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Yaku iyalai da ‘yan uwa da abokai da kuma sauran jama’ar mazabar Irepo a majalisar Tarayya.
“Cikin kunci ina mai sanar da ku rasuwar mahaifiyata, Alhaja Nusiratu Ajike wacce ta rasu da safiyar yau.
“Mahaifiyata ita ce silar kwarin gwiwa ta, ga ta da tausayi da taimako, za mu yi kewar rashinta da ma sauran mutanen wannan yanki.”

Ya ce marigayiyar ta sadaukar da rayuwarta wurin yi wa mutane hidima da kuma zama abin koyi ga mutane da dama, cewar Legit.ng.

Ya ce mahaifiyarsu ta sadaukar da rayuwarta wurin yi wa mutane bauta

Ya kara da cewa:

“Ta sadaukar da rayuwarta wurin yi wa jama’a hidima wacce ta kasance abin koyi ga ‘yan baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

"A matsayinta na musulmar kirki, za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, za a sanar da lokaci da kuma wurin da za a gabatar da sallar jana’izar.”

A karshe ya godewa ‘yan uwa da abokan arziki da ma jama’ar yankin ganin yadda suke musu addu’a bayan rasuwar mahaifiyar tasu.

Hajjin 2023: Maniyaciyyar Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya A Saudiyya

A wani labarin, daya daga cikin mahajjatan birnin Tarayya Abuja, Hajiya Amina Yunusa ta riga mu gidan gaskiya a Saudiyya.

Marigayiyar ta rasu ne yayin aikin hajjin baba bayan fama da jinya Makkah da ke Saudiyya.

Hukumar alhazan jihar ne ta bakin daraktanta, Abubakar Evuti ya sanar da rasuwar marigayiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel