Gwamna Zulum Ya Samar Da Motoci 300 Domin Kai Manoma Gonakinsu a Borno

Gwamna Zulum Ya Samar Da Motoci 300 Domin Kai Manoma Gonakinsu a Borno

  • Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nemar wa manoman jihar hanyar zuwa gonakinsu cikin sauƙi
  • Gwamnan ya samar da motoci 300 da za su yi jigilar sama da manoma 10,000 zuwa gonakinsu a lokacin damina
  • Zulum ya ce an samar da motocin ne domin rage raɗaɗin da manoman su ke ji a dalilin tsige tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, a ranar Talata ya samar da motoci 300 da za su riƙa jigilar sama da manoma 10,000 zuwa gonakinsu a ƙaramar hukumar Damboa.

Hakan na zuwa ne bayan ƴan ta'addan Boko Haram sun kai mabambantan hare-hare har guda biyu a ƙaramar hukumar satin da ya gabata.

Gwamna Zulum ya samar da motocin jigilar manoma
Gwamna Zulum ya ce manoman za su rage radadin cire tallafin man fetur Hoto: @NTANewsNow
Asali: Twitter

Gwamnan wanda ya duba hanyar kafin zuwan manoman, ya tsaya domin tattaunawa da sojoji kan yadda jigilar manoman za ta tafi yadda ake so, jaridar Daily Trust ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Mutum Uku da Ake Zargi da Hannu a Sace Babban Malamin Musulunci a Najeriya

Motocin za su kawo sauƙi ga manoma, Zulum

Ya kuma ƙara da cewa motocin za su rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi ga manoman, rahoton NTA ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Domin rage raɗaɗin da manoma su ke ciki, gwamnatin jiha ta yanke shawarar samar da motocin da za su riƙa kai manoma gonakinsu ba tare da ko sisi ba a lokacin wannan daminar."
"A nan wannan babban titin hanyar Maiduguri -Damboa, an samar da motoci 15 da motocin haya 30 domin samar da hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙungiyoyin sufuri na jiha. A jimlace motoci 60 za a samar a wannan hanyar domin kai manoman gonakinsu."
"Ina roƙon manoman da su bayar da cikakken goyon baya ga sojojin Najeriya, suna wajen nan ne domin su kare ku da samar da tsari wanda zai tabbatar da an yi jigilarku cikin tsanaki."

Kara karanta wannan

Yariman Bakura Ya Sanya Labule Da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Wata Alfarma 1 a Madadin 'Yan Bindiga

Legit Hausa ta samo jin ta bakin wani mazaunin garin Biu a jihar Borno wanda ya nemi a sakaya sunansa, wanda ya yaba da wannan namijin ƙoƙarin da gwamnan ya yi.

Ya bayyana cewa gwamnan ya yi abinda a yaba domin mutanen da aka samar da motocin dominsu suna cikin wani yanayi saboda halin da yankunansu su ke ciki.

A cewarsa samar da motocin za su ƙara sauƙaƙa rayuwa ga mutanen da za su amfana da su, inda ya yi kiran cewa yakamata motocin a samar da su a dukkanin yankunan jihar ta Borno.

Tsadar Mai Ta Sanya An Koma Amfani Da Keke a Borno

A wani labarin kuma, tsadar da man fetur ke tsulawa ya sanya al'ummar jihar Borno sun nemo hanyoyin da za su nema wa kansu sauƙi.

Mazaunan jihar ta Borno dai sun koma amfani da kekunan hawa domin yin zirga-zirgarsu saboda yadda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel