Fastoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani Da Aka Yi A Sweden

Fastoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani Da Aka Yi A Sweden

  • Limaman majami'u a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani a kasar Sweden
  • Rabaran Dakta James Noble da Fasto Yohanna Buru su suka bayyana haka a Kaduna yayin jaje ga 'yan uwa Musulmai
  • Lamarin wanda ya faru a ranar sallah a birnin Stockholm ya jawo cece-kuce a tsakanin al'ummar duniya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Wasu limaman majami'a a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani mai girma a kasar Sweden.

Lamarin ya faru a ranar sallah a kasar Sweden wanda ya jawo cece-kuce a duniya baki daya.

Fastoci a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani a Sweden
Fastoci A Arewa Sun Bayyana Bacin Ransu kan Kona Alkur'ani. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Rabaran Dakta Noble James da Fasto Yohanna Buru sun bayyana kaduwarsu yadda gwamnatin kasar ta bar hakan ta faru.

Fastocin sun bayyana Musulunci a matsayin addini mai son zaman lafiya

Dukkan Fastocin sun bayyana cewa addinin Musulunci na koyar da zaman lafiya da kaunar juna, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Jam'iyyar PDP Ta Yabi Tinubu Kan Matakan Da Ya Ke Dauka, Ta Ce Ya Yi Bajinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kara da cewa sun shirya don kare martabar Alkur'ani a ko yaushe kuma a ko ina.

Sun kirayi shugabannin duniya musamman kungiyar Nahiyar Turai da su dau mataki tare da kamo masu laifin.

Don neman yafiya da zaman lafiya, sun ba wa Larabawa da sauran Musulmin duniya hakuri akan abinda ya faru, cewar Tribune.

Sun bukaci hukumomi su dauki mataki akan Sweden da masu laifin

Sun roki Musulmai da su kwantar da hankalinsu don gudun daukar fansa, inda suka tabbatar cewa za su ci gaba da wa'azin zaman lafiya.

Lamarin ya faru ne inda aka gano mutane biyu suna kona Alkur'ani a wajen masallacin Stockholm da goyon bayan kotun kasar.

Fastocin sun bukaci da a dauki matakin dakile faruwar hakan a gaba, inda suka nemi a zauna lafiya a tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: UN Ta Fadi Irin Kuncin da 'Yan Arewa Suka Shiga Biyo Bayan Matakin Tinubu Na Cire Tallafin Mai

Sallah: CAN Ta Taya Musulmai Murna, Ta Ce ‘Dukkan Mu Yan Uwan Juna Ne’

A wani labarin, Kungiyar CAN ta taya 'yan uwa Musulmi murnar zagayowar bikin sallah inda ta ce duk 'yan uwan juna ne.

Kungiyar ta nemi Musulmai su yi addu'a don samun zaman lafiya da kaunar juna a kasar Najeriya.

Shugaban kungiyar CAN, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a ranar Talata 27 ga watan Yuni a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel