'Yan Kalare: 'Yan Sanda Za Su Koyawa Tubabbun Tsageru Sana'a a Rage Kashe Wado

'Yan Kalare: 'Yan Sanda Za Su Koyawa Tubabbun Tsageru Sana'a a Rage Kashe Wado

  • Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta kirkiro shirin koyawa tubabbun yan kalare sana'o'i domin samun zaman lafiya a jihar
  • A karon farko shirin zai fara ne da tubabbun yan kalare 20 domin koya musu sana'o'i daban daban da za su samu abin dogaro da kai
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi karin haske kan irin sana'o'in da za su koya wa matasan da kuma yadda shirin zai cigaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Biyo bayan kira da rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta yi ga yan kalare a kan su tuba, ta sanar da tuban matasa sama 200.

Domin tabbatar da tuban na su, rundunar ta yi hadaka da kungiyoyin sa kai domin koya musu sana'o'i.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Majalisa ta bukaci samar da jami'an tsaron hadin gwiwa a Niger

Police IG
Yan sanda za su koyar da matasa sana'o'i saboda rage ta'addanci. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Hayatu Usman ne ya tabbatar wa manema labarai hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sanda ya yi jawabin ne a lokacin da ake kaddamar da shirin koya musu sana'o'in a ranar Laraba.

Wadanda za su tallafawa shirin 'yan kalare

Rahoton jaridar Aminiya ya nuna cewa za ayi hadakar ne da rundunar 'yan sandan jihar da wata kungiya mai zaman kanta, Trive Trek Enterprise Center tare da tallafin gwamantin jihar.

Shugaban kungiya mai zaman kantan, Alhaji Aliyu Babangida National ya ce sun shigo cikin lamarin ne domin samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Sana'o'in da za a koyawa 'yan kalare

Daga cikin sana'o'in da za a koya wa tubabbun matasan sun hada da aikin gyaran wuta, kafa kyamarar tsaro ta CCTV da kuma kafa na'urar wuta mai amfani da hasken rana.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba yayin da 'yan banga suka bindige babban jami'in ɗan sanda a Taraba

Ana fatan shirin zai taimaka wajen rage aikin barna da ta'addanci a jihar Gombe musamman idan aka samu karin matasa da suka shiga shirin.

Domin kwamishinan yan sanda a jihar ya koka kan yadda matsan suke kara komawa ayyukan daba koda an kaisu gidan gyaran hali.

Adadin matasan da za a koyawa sana'a

A cikin matasan da suka ajiye makamai sama da 200 za a dauki 20 ne domin fara koya musu sana'o'in a halin yanzu.

Sai dai kwamishinan yan sandan ya yi kira ga suaran kungiyoyi kan shigowa cikin lamarin domin kara daukan matasan da suka tuba a koya musu sana'o'i.

Kokarin gwamnatin Gombe kan samar da tsaro

Mai taimakawa gwaman jihar Gombe kan harkokin tsaro, AIG Zubairu Mu'azu ya ce gwamnatin jihar tana kokarin wurin ganin rage ayyukan barna da matasan ke yi.

A cewar AIG Mu'azu a halin yanzu suna ƙoƙarin kammala wata makaranta da za ta rika bawa matasan horo kan sana'o'i a garin Boltingo.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC ya dauki sabon mataki domin kawo karshen wahalar man fetur

An kashe wata mata a ihar Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa, rundunar 'yan sanda sun tabbatar da kisan gilla ga wata dattijuwa a unguwar Jekadafari da ke birnin Gombe

An yi wa marigayiyar mai suna Aishatu Abdullahi yankan rago ne yayin da 'yan ta'adda su ka shiga gidan ta a daren jiya Juma'a da misalin karfe 8:00.

Asali: Legit.ng

Online view pixel