An Ba FG Awanni 72 Ta Kama Asari Dokubo Kan Barazanar Da Ya Yi Wa Inyamurai

An Ba FG Awanni 72 Ta Kama Asari Dokubo Kan Barazanar Da Ya Yi Wa Inyamurai

  • Ana ta kiraye-kiraye kan gwamnatin tarayya ta kama tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo
  • A farkon watan Yuni, an gano Dokubo a cikin wani bidiyo da ya yadu rike da bindigar AK-47 yana barazanar shafe inyamurai
  • A bidiyon, ya yi masu ba'a, yana mai cewa ba don Turawa da suka shigo lamarin ba da har yanzu yana nan yana siyar da su a matsayin bayi

An matsawa gwamnatin tarayya kan ta kama tsohon shugaban tsagerun yan bindigar Neja Delta dan tawaye Mujahid Asari-Dokubo.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, kungiyar kare hakkin dan adam ta Najeriya (HURIWA) ce ta yi kiran a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni.

Shugaban kasa Bola Tinubu da Asari Dokubo
An Ba FG Awanni 72 Ta Kama Asari Dokubo Kan Barazanar Da Ya Yi Wa Inyamurai Hoto: Bola Ahmed Tinubu and @redcap_blondie
Asali: UGC

An ba FG awanni 72 ta kama Asari Dokubo

Shugaban kungiyar HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya ce gwamnatin tarayya na da awanni 72 ta kama Dokubo ko kuma su yi zanga-zanga a fadin kasar harda binin tarayya.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Jam'iyyar PDP Ta Yabi Tinubu Kan Matakan Da Ya Ke Dauka, Ta Ce Ya Yi Bajinta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda jaridar Daily Independent ta rahoto, ya ce:

“Ya zama dole rundunar tsaron farin kaya ko hukumar tsaro masu alaka su kama Asari-Dokubo kan alakarsa da yan bindiga da ba a san ko su waye ba a kudu maso gabas.
"Ya zama dole gwamnatin Najeriya ta kama Asari Dokubo ko kuma a kaikaice gwamnatin tarayya na nufin matasan Inyamurai, masoyan inyamurai da dukkan kungiyoyi da ke goyon bayan ci gaban Inyamurai su fara zanga-zangar lumana a lokaci guda.
“HURIWA na ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu awanni 72 domin ya yi umurnin kamawa da binciken Asari Dokubo kan zargin alakarsa da yan bindiga da ba a san ko waye ba a kudu maso gabas ko kuma HURIWA za ta kira mambobinta domin yin zanga-zanga a Abuja a mako mai zuwa kan lamarin."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Kungiyar ta bayyana cewa bai kamata a bar rashin doka ya yadu ba sannan ta bukaci hukumomin tsaro da kada su yi kamar basu san hatsarin da ke tattare da abun da Dokubo ya yi ba.

Barazanar da HURIWA ta yi da neman a kama Dokubo ya kasance ne kan bidiyonsa da ya yadu inda ya yi barazana ga Inyamurai yayin da yake rike da bindigar AK-47 a bidiyon.

Asari Dokubo ya shawarci Tinubu da kada ya saki Nnamdi Kanu

A gefe guda, mun ji a baya cewa dan fafutuka, Asari Dokubo ya shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya kuskura ya saki shugaban kungiyar awaren IPOB.

A cewar Dokubo, sakin Nnamdo Kanu ba zai haifar da 'ya'ya masu idanu ba domin zai kara tayar da hankali a kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel