Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

  • Mutane shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani harin bam da 'yan Boko Haram suka kai musu a Borno
  • An bayyana cewa 'yan ta'addan sun binne wani abin fashewa ne akan wata hanyar kauye da jama'a ke yawan bi
  • Hanyar da aka kai harin wato tsakanin Konduga zuwa Bama, ta dauki lokaci mai tsawo ba tare da farmakin Boko Haram ba

Maiduguri, jihar Borno - Akalla mutane shida ne suka mutu a Borno lokacin da wata motar haya ta bi ta kan wani boyayyen abin fashewar da 'yan ta'addan Boko Haram suka binne a kan hanya.

Lamarin dai ya faru ne a kan hanyar karkara da ke tsakanin Bama zuwa Kawuri a karamar hukumar Konduga, inda jama’a suka saba bi domin zuwa wasu sassa na jihar, kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a Tuwita.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

'Yan Boko Haram sun halaka mutane 6 a Borno
Bam da 'yan Boko Haram suka binne kan hanya ya janyo mutuwar mutane shida. Hoto: @profZulum
Asali: Twitter

A tsakiyar hanya Boko Haram suka dana bam din

Majiyoyi sun ce, Alhaji Ari Hajja Fusam, Amir Jaysh na kungiyar Jama’ati Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad ne ya dauki nauyin kai harin, daga sansanin Gaizuwa da ke da nisan kilomita kadan daga wurin da lamarin ya faru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zagazola Makama, wanda kwararren mai sharhi ne a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya yi bayani kan lamarin.

Zagazola ya bayyana cewa daya daga cikin motocin, wata mota kirar Toyota starlet da ta dawo daga jihar Adamawa, ta taka bam din, inda duka fasinjoji biyar dake cikinta suka rasu.

An kai shekaru shida ba tare da harin 'yan Boko Haram ba a yankin

Zagazola ya kara da cewa daga baya direban wanda ya samu munanan raunuka ya rasu bayan sa’a daya a wani asibiti da ke cikin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Hanyar da ke tsakanin garin Bama zuwa Konduga ta kasance cikin zaman lafiya da lumana, domin ba a samu wani hari ba a cikin shekaru 6 da suka gabata ba.

A cewar Zagazola, sai yanzu ne dai kuma da maharan suka yanke shawarar tayar da bama-bamai a kan titin.

Sojojin sama sun yi luguden wuta kan sansanonin 'yan ta'adda

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan luguden wutar da jami'an sojin sama suka yi wa 'yan Boko Haram a maboyarsu.

An bayyana cewa luguden wutar da aka yi wa mayakan na Boko Haram, ya yi fata-fata da maboyarsu a yayin da da yawa daga cikinsu suka sheka barzahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel