“Na Nemi a Kawo Mani Karamar Yarinya”: Matar Aure Ta Koka, Ta Nuna Yarinyar Da Surukarta Ta Bata

“Na Nemi a Kawo Mani Karamar Yarinya”: Matar Aure Ta Koka, Ta Nuna Yarinyar Da Surukarta Ta Bata

  • Wata yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta nunawa duniya yarinyar da susrukarta ta kawo mata
  • A cewarta ta fada ma uwar mijinta cewa ta samo mata yar karamar yarinya da za ta dunga taimaka mata amma sai labari ya sha banban
  • Sai dai kuma, mutane da dama sun hango dalilin da yasa surukar ta zabo wannan yarinya yayin da suka shawarci matar

Wata matar aure yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya kan yarinyar da uwar mijinta ta kawo mata.

Ta wallafa wasu jerin bidiyoyi na karamar yarinyar tana bacci tare da jinjirinta a kan gado.

Yara suna bacci a gado
“Na Nemi a Kawo Mani Karamar Yarinya”: Matar Aure Ta Koka, Ta Nuna Yarinyar Da Surukarta Ta Bata Hoto: @asa_marshal
Asali: TikTok

Matashiyar ta bukaci cewa uwar mijinta ta samo mata karamar yarinya da za ta taimaka mata da aikace-aikacen gida.

Sai dai kuma, yarinyar da aka kawo mata ta fi bukatar taimakonta maimakon ita ta taimaka mata.

Kara karanta wannan

“Na Zabi Nutsuwa”: Matashiya Da Ta Shafe Shekaru 7 Tan Soyayya Da Namiji Ta Rabu Da Shi Watanni 3 Bayan Sun Yi Aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi cece-kuce kan bidiyon yayin da jama'a suka bayyana ra'ayoyinsu kan zabin uwar mijin tata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga bidiyon

Gift Scotland ta ce:

"Za ki so ace karamar diyarki ko danki ya tafi yin aikatau a gidan wani a lokacin da ita kanta yarinyar ke bukatar ace tana makaranta?"

Efemena Joy Egbe ta ce:

"Ki barta ta ji tamkar a gidansu take za ta girma da son ahlinki sannan ta kula da 'ya'yanki."

harbezzybabe ta ce:

"Na fara zama da antina tun ina da shekaru 3 yanzu shekaruna 19 kuma ba za ka banbance tsakanina da yayanta ba....Kawai ki kula da ita kuma za ki ji dadinta."

Aiden19 ta ce:

"Ta yi abun da ya dace kafin ta aiko wacce za ta fatattake ki daga gidan mijinki, don Allah ki kula da wannan da kyau za ki ji dadinta."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Shiga Yanayi Bayan Saurayinta Ya Gudu Saboda An Yanke Mata Kafa

Ujunwa Ikueze ta ce:

"Na fara zama da antina ina da shekaru 7 yanzu shekaruna 22 nice Hajiya a gidan ki kula da ita za ki ji dadinnta idan ta girma."

Matashiya ta rabu da mijinta da suka shekara 7 suna soyayya watanni 3 bayan aurensu

A wani labari na daban, wata matashiya ta ba da labarin yadda suka shafe tsawon shekaru bakwai suna soyayya da mijinta amma suka rabu bayan watanni uku kacal da aurensu.

A cewarta, ta zabi nutsuwar zuciyarta ne shiyasa ta fice daga auren amma tabbass akwai ciwo a mutuwar aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel