Matar Da Ta Shafe Shekaru 7 Tana Soyayya Da Namiji Ta Rabu Da Shi Watanni 3 Bayan Ya Aure Ta

Matar Da Ta Shafe Shekaru 7 Tana Soyayya Da Namiji Ta Rabu Da Shi Watanni 3 Bayan Ya Aure Ta

  • Wani dan gajeren bidiyon TikTok ya nuno wata yar Najeriya wacce ta ce ta shafe tsawon shekaru bakwai tana soyayya da namiji kafin ta aure shi
  • Amma kuma matashiyar ta kuma bayyana a bidiyon cewa ita da mijin nata basa tare domin aurensu ya mutu
  • Matashiyar ta ce ta zabi nutsuwar zuciyarta sama da auren, tana mai cewa alaka na soyayya na iya zama tamkar yaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya yar Najeriya ta bayyana cewa ita da mijinta basa tare watanni uku bayan sun yi aure.

A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok, @bolaghold ta ce ta yanke shawarar barin gidan aurenta domin ta ci gaba da samun nutsuwar zuciya.

Ta ce ta zabi zaman lafiya
Matar Da Ta Shafe Shekaru 7 Tana Soyayya Da Namiji Ta Rabu Da Shi Watanni 3 Bayan Ya Aure Ta Hoto: TikTok/@bolaghold
Asali: TikTok

Matashiyar ta bayyana a cikin wani bidiyon TikTok cewa abu ne mai matukar zafi barin gidan aurenka, musamman kasancewar ita da mutumin sun shafe tsawon lokaci suna soyayya.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Shiga Yanayi Bayan Saurayinta Ya Gudu Saboda An Yanke Mata Kafa

Yar Najeriya ta br gidan aurenta bayan watanni uku

Ta bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru bakwai suna soyayya kafin suka shiga daga ciki a 2022. Ta bayyana cewa yanzu shekara daya kenan da ta bar gidan aurenta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Soyayya na iya zama tamkar yaki wasu lokutan. Kuma ina yawan tambayar kaina a ina ne na yi kuskure a so."

A wani bidiyon, an gano matar sanye da kayanta na aure. An gano ta cikin doguwar riga irin na amare da kuma saki. Ta ce ta la'anci ranar 26 ga watan Yuni, wanda a wannan rana ne ta yi aure.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@aderonkeCAN_makeoverz ta tambaya:

"Ta yaya kika iya ci gaba da harkoki? Saboda nima ina cikin irin wannan yanayi. Ina tsoron fecewa saboda bani da karfin aljihu da zan iya dogaro da kaina tukuna."

Kara karanta wannan

“Yar'uwata Ce Ta Nemi Na Yi Haka”: An Sha Yar Dirama Yayin da Miji Ya Dirka Wa Kanwar Matarsa Ciki, Ta Ki Zubarwa

@user9032291651472 ta ce:

"Ku zo ku yi bayanin abun da ke cikin aure. Don Allah soyayyar shekaru 7 kawai sai a rabu batan watanni 3 da aure?"

@Nthabiseng ta ce:

"Ina cikin wani yanayi. Ina a auren watanni 5, amma ji nake yi kamar na fice."

Yayata ta sa ni kwanciya da shi: miji ya dirkawa kanwar matarsa ciki, ta ki ta zubar

A wani labari na daban, wasu ma'aurata na cikin tsaka mai wuya bayan miji ya dirkawa kanwar matarsa ciki.

Kanwar da aka yi wa ciki ta ce sam ba za ta zubar da shi ba domin a cewarta sau uku kenan yana dirka mata ciki da sa ta zubarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel