Bayan Makonni 4, Buhari Ya Gaza Zaman Daura, Ya Fadi Dalilin Tserewa Daga Mahaifarsa

Bayan Makonni 4, Buhari Ya Gaza Zaman Daura, Ya Fadi Dalilin Tserewa Daga Mahaifarsa

  • Maganar da ake yi a yanzu Muhammadu Buhari bai cika alkwarinsa na zama a garin Daura ba
  • Mutane su na damun tsohon Shugaban kasar a lokacin da yake bukatar ya samu hutu a kauyensu
  • Garba Shehu ya shaida cewa Muhammadu Buhari ya yi nisa, amma dai bai fadi inda ya koma ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A halin yanzu Muhammadu Buhari ya bar mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina, bayanin nan ya fito ne daga bakin Garba Shehu.

A jawabin da ya fitar a shafinsa na Twitter a yammacin Alhamis, Malam Garba Shehu ya ce tsohon shugaban Najeriyan ba ya garin Daura.

Da yake bayani, mai magana da yawun bakin Muhammadu Buhari bai yi bayanin inda ya koma ba, sai dai ya fadi abin da ya jawo hakan.

Kara karanta wannan

‘Na Shekara 4 Da Makanta’: Labarin Makaho Da Ke Amfani Da Wayar ‘IPhone’ Ya Girgiza Intanet

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari da iyalinsa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Bayan wata daya ya na zaune a cikin mutanensa, sai ga shi labari ya zo cewa ya tattara ya bar gonarsa da dabbobinsa da yake sha’awa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana nan a gidan jiya

Garba Shehu ya nuna dattijon bai samun yadda yake so a garin na Daura, duk da ya bar kan mulki, mutane su na yawan kai masa ziyara.

Hadimin ya ce mai gidansa ya sake lulawa zuwa wani wuri mai nisa domin ya yi rayuwa tsit.

Buhari ya koka da cewa masu ziyara su na yi masa cin-cin-rindo dare da rana, abin da ba zai so ba a lokacin da yake kokarin samun hutu.

Jawabin Garba Shehu

"Dama ya tafi Daura ne da nufin ya samu irin rayuwar da yake so ta rashin hayaniya, amma sai ya fahimci ba haka lamarin yake ba.
Masu ziyara su na durowa dare da rana, sai ya tafi zuwa wani wuri mafi nisa.

Kara karanta wannan

An Gano Motar N55m a Delta Bayan Ɓarawo Ya Tsere da Ita Daga Hawa Ɗani Abuja

Abin da yake so shi ne a kyale shi ya samu hutun da yake bukata kuma gwamnatin Tinubu ta ji dadin aiki, ta cika alkawuran da ta dauka.

- Garba Shehu

Buhari ya tafi Nijar?

Tun kafin ya bar fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa a Mayun 2023, Buhari ya yi alkawarin cewa zai zauna na watanni a kauyensu.

Legit.ng Hausa ta taba kawo rahoto cewa tsohon sojan ya ce idan har mutane su ka dame shi, zai tsallaka zuwa Nijar da ke iyaka da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel