Yar Najeriya Da Ke Talla a Titi Ta Koma Turai, Rayuwarta Ta Sauya Gaba Daya

Yar Najeriya Da Ke Talla a Titi Ta Koma Turai, Rayuwarta Ta Sauya Gaba Daya

  • Wata yar Najeriya da ta sha wahala sosai a matsayin yar talla ta yi nasara a rayuwa bayan ta koma Turai ta kuma samu aiki mai kyau
  • Matashiyar ta nuna yadda talla na tsawon awanni ya yi mata illa da bar mata rauni daban-daban a tafukan kafafunta
  • Yan Najeriya da dama da suka kalli bidiyon yadda rayuwarta ta sauya sun ce ta karfafa masu gwiwar cewa kada su yanke kauna a rayuwa

Wata matashiya da ke tallan lemukan kwalba a Najeriya na tsawon awanni cikin zafin rana ta samu sauyi a rayuwa.

A wani mataki a bidiyon da aka wallafa a TikTok, matashiyar @sinatu26 ta nuna yadda talla na tsawon awanni ya lalata mata tafukan kafafunta. kafafuwan nata na dauke da raunuka iri-iri.

Matashiya ta sauya bayan ta sha fama a rayuwa
Yar Najeriya Da Ke Talla a Titi Ta Koma Turai, Rayuwarta Ta Sauya Gaba Daya Hoto: @sinatu26
Asali: TikTok

Sauyawar budurwa yar Najeriya mai ban mamaki

Kara karanta wannan

"Yana Ƙaunata Duk da Banda Hali" Wata Mata Ta Saki Zafafan Hotunanta da Ƙatoton Mijinta

Matashiyar ta taba yin talla a wajen wani shagali. Yan sakanni a bidiyon, sauyawarta ya ba mutane da dama mamaki yayin da aka ajiye ta a wani filin jirgin sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tafi kasar waje sannan ta fara aiki. Kayan aikin da ke sanye a jikinta ya nuna cewa ta zama malamar jinya. Mutane da dama da suka ga yadda rayuwarta ya sauya sun tayata murna Kalli bidiyon a kasa:

.Jama'a sun yi martani:

Shodimu Titilope Mar ta ce:

"Ubangiji da ya sauya labarinki zuwa na farin ciki zai sauya nawa nima."

wunmiopeyemi39@gmail.com ta ce:

"Ina maki addu'a daga kasan zuciyata za ki yi nasara a rayuwa da yardar Allah."

Olori Guarantor ta ce:

"Na tayaki murna, na yaba ma Ubangiji a rayuwarki."

Samsudeen Olapade ya ce:

"Wannan sauyawar na da girma."

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Ajiye Girman Kai, Ta Isa Gaban Saurayinta Da Zobe Domin Neman Aurensa, Hotuna Sun Yadu

olaponleogunsuada ya ce:

"Awwwwww na tayaki murna."

user1134411451161 ya ce:

"Na tayaki farin ciki sosai."

Maimay Temisan Abimbola ta ce:

"Wow na tayaki murna ya bani karfin gwiwa...Irin babu yanayi da yake madawwami."

Delight119 ya ce:

"Haaaaaa idan kin yi nasara wanene ni da ba zan gwada sa'ata ba."

Bayan hade asusun banki suna tara kudi da mijinta, mata ta fece da kudaden

A wani labari na daban, wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel