Matan Zamani: Bayan Hade Asusun Banki Suna Tara Kudi Da Mijinta, Mata Ta Fece Da Kudaden

Matan Zamani: Bayan Hade Asusun Banki Suna Tara Kudi Da Mijinta, Mata Ta Fece Da Kudaden

  • Wata mata yar Najeriya ta fece bayan ta yashe gaba daya kudaden da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta
  • An tattaro cewa na kwashi mutumin zuwa asibiti inda a nan ne ya sanar da abokai da yan uwansa abun da ake ciki
  • Matar mutumin ta fatattaki abokansa ta hanyar nuna masu mugun hali, sannan yanzu ta fece

Wani labari da ke yawo a Twitter ya bayyana cewa wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Mace da namiji da kuma tsabar kudi
Matan Zamani: Bayan Hade Asusun Banki Suna Tara Kudi Da Mijinta, Mata Ta Fece Da Kudaden Hoto: Getty Images/Westend61 and Bloomberg.
Asali: Getty Images

Koda dai ba a ambaci yawan kudin da ke asusun ba, amma dai an ce mijin matar ya shiga wani yanayi.

Kara karanta wannan

"Yana Ƙaunata Duk da Banda Hali" Wata Mata Ta Saki Zafafan Hotunanta da Ƙatoton Mijinta

Matar aure ta kwashe gaba daya kudaden da ke cikin asusunta da na mijinta

Da take ba da labarin a Twitter, @ps_wears ta ce ita da mutumin abokai ne lokacin da ya so auren matar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta bayyana yadda matar mutumin ta yi nasarar korarta a matsayin kawarsa ta hanyar dagewa kan cewa kada a gayyaceta zuwa wajen aurensu.

Da ta fuskanci haka, sai @ps_wears ta ki halartan bikin da gangan.

Wani bangare na labarin na cewa:

"Na daina nemansa, ina mutunta iyaka sosai. Yan shekaru bayan nan aka kira ni daga asibitin koyarwar cewa an kwantar da shi sannan ya bukaci a neme ni. Ban so zuwa ba. Na dauki wayata sannan na kira wnai abokinsa da na sani. Chinedu, me yasa suke kirana daga asibiti.
"A nan ne na fara jin labari, muka kira sauran abokai sannan muka hadu a asibitin. Matar ta kori abokansa gaba daya sannan ta tsere da kudadensu asusunsu na hadin gwiwa."

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Ajiye Girman Kai, Ta Isa Gaban Saurayinta Da Zobe Domin Neman Aurensa, Hotuna Sun Yadu

Duba cikakken labarin:

Jama'a sun yi martani

@Funmiscute ta ce:

"Na san wani da matarsa ta dauki wayarsa sannan ta nemi sanin su wanene lambobin da ke wayar, ta sa ya goge lambobi tare da toshe lambobin mutane da dama. Shi ya fada mun da dabara. Ana bukatarsa don wani aiki amma bai yi ba saboda matar ta hana. Wannan mutum ne da matarsa ke dauke da lambobin duk wasu maza kuma ya sani."

@b_tifetigress ta ce:

"Baaba wannan ya sa ni bakin ciki sosai. Ya kamata mutumin da ka aura ya zama wanda zai ingantaka ba karar da kai ba."

@abu_omya ya ce:

"Wannan labari naki na fasa kwanya don Allah."

Budurwa ta nemi auren saurayinta a bainar jama'a, hotuna sun yadu

A wani labari na daban, wata matashiya ta girgiza intanet bayan ta isa gaban saurayinta rike da zoben alkawari.

Matashiyar budurwar dai ta nemi saurayin ya aureta ba tare da la'akari da ko hakan ya saba al'ada ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel