An Bude Iyakar Legas Domin Shigo da Motoci, Gwamnati Ta Yi Watsi da Tsohon Tsari

An Bude Iyakar Legas Domin Shigo da Motoci, Gwamnati Ta Yi Watsi da Tsohon Tsari

  • Gwamnatin tarayya tayi na’am da bude iyakokin kasa domin a rika shigo da abubuwan hawa
  • Wannan dama da aka bada ta shafi iyakar Seme, ‘yan kasuwa za su iya shigo da motoci daga yanzu
  • Tun a lokacin gwamnatin baya aka aika takarda zuwa FEC, an saurari koken ‘yan kasuwa da kwastam

Abuja - Ganin korafi sun yi yawa, Gwamnatin tarayya ta amince a bude wata daga cikin iyakar kasar nan da nufin shigo da kaya daga kasashen waje.

A ranar Alhamis aka samu labari daga Vanguard cewa an bada umarnin bude iyakar nan ta Seme da ke garin Legas da nufin a shigo da abubuwan hawa.

Darektan tafiye-tafiye ta titi a ma’aikatar sufurin tarayya, Ibrahim Musa ya bayyana cewa za a dawo shigo da motoci da duk abubuwan hawa ta iyakar.

Kara karanta wannan

Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

Motoci
Motoci a kasar waje Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ibrahim Musa ya yi jawabi ne a wajen taron da kuniyar ECOWAS ta shiryawa jami’an Najeriya da Benin a sakamakon koke-koke da ‘yan kasuwa su ke yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce masu shigo da kaya ta iyakar Seme sun kai kuka, don haka aka dauki wannan mataki.

'Yan kasuwa sun kai kuka

Darektan zirga-zirgar ya shaidawa jami’an ECOWAS da su ka ziyarci kan iyakar Seme-Krake cewa ya san lokacin da ‘yan kasuwa su ka nemi alfarma.

Kafin Muhammadu Buhari ya bar mulki, masu kasuwanci a yankin sun roki karamar Ministar sufuri ta amince a rika shigo da kaya ba tare da wani kaidi ba.

A cewar Ibrahim Musa, tsohuwar Ministar ta umarce su da su rubuta takarda a kan batun, kuma su aikawa gwamnati, a karshe aka yi la’akari da bukatar.

Kara karanta wannan

Tserewa Zai Yi: Gwamnati Ta Haskawa Kotu Hadarin Bada Belin Godwin Emefiele

Kwastam ta ga kudi ya ja baya

Shugaban hukumar kwastam na iyakar, Dera Nnadi ya shaida cewa kudin-shigan da su ke samu ya ragu da aka haramta shigo da motoci ta iyakokin kasa.

Dera Nnadi ya yi bayanin yadda tsohuwar Minista ta amshi koke-kokensu, ta kai maganar zuwa gaban FEC domin ganin gwamnatin tarayya ta bude iyakoki.

Tun a lokacin, ma’aikatar ta sanar da majalisar FEC ta amince da bukatun da su ka gabatar.

Richard Montgomery ya yabi Tinubu

An rahoto Jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Montgomery ya ce Duniya ta na lura da tsare-tsaren da Shugaba Bola Tinubu yake kawowa da ya hau mulki.

Bayan ya zauna da Kashim Shettima a jiya, Montgomery ya ce cire tallafi da kuma gyara tsarin kudin kasar waje za su taimaka wajen jawo hannun jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel