Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

  • Richard Montgomery ya yi zama na musamman da mataimakin shugaban kasa a Aso Rock
  • Jakadan Birtaniyan ya yabi Gwamnatin Bola Tinubu, ya ce matakan da ta dauka sun yi daidai
  • Montgomery ya ce tattalin arziki zai bunkasa a dalilin cire tallafin fetur da karya Darajar Naira

Abuja - Jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Montgomery, ya ce Duniya ta na lura da manya kuma muhimman matakan da Bola Tinubu yake dauka.

Vanguard ta ce Jakadan kasar Birtaniyan ya yi wannan bayani ne da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ya yi zama da Kashim Shettima.

Montgomery ya hadu da Sanata Shettima a fadar shugaban kasa da ke garin Abuja. A halin yanzu Mai girma Bola Ahmad Tinubu ya yi tafiya zuwa ketare.

Shugaban kasa Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jakadan ya fadawa ‘yan jarida cewa cire tallafin man fetur da kawo gyara wajen harkar canjin kudi da Bola Tinubu ya yi za su bunkasa harkar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Gana da Jakadan Burtaniya a Villa, Abinda Suka Tattauna Ya Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Montgomery ya ce ya zanta da mataimakin shugaban kasan ne a kan abubuwan da su ka shafi kasuwanci, cinikayya, tsaro da alakar tattali.

Jawabin Richard Montgomery

“Mun tattauna doguwar alakar da ke tsakanin Birtaniya da Najeria; Akwai bangarorin da mu ke da sha’awa tare; daga ciki har da tarihin dangantakar cigaba.
Akwai kyawawan tsare-tsaren kasuwanci da zuba hannun jari, kuma mun hada-kai a bangaren tsaro.
Mu na da kyakkyawan tattaunawa a kan tattalin arziki. Manyan matakan da gwamnatin nan ta dauka su na da muhimmanci sosai, ana lura da su a Duniya.
Cire tallafi; gyara tsarin kudin kasar waje, wadannan duk za su taimaka wajen jawo hannun jari." - Richard Montgomery

Daily Trust ta rahoto Jakadan ya na mai yabon matakan da Gwamnatin Tinubu ta fara dauka a ofis. Labarin ya zo a tashar talabijin na kasa ta NTA.

Kara karanta wannan

Jirgin Bola Tinubu Ya Sauka a Faransa, An Ji Ranar da Shugaban Kasa Zai Dawo Najeriya

Jakadan ya amsa tambaya a game da matakin da gwamnatin Birtaniya na hana iyalan dalibai zuwa kasarta, ya ce ba su tabo batun da Shettima ba.

IMF ta yabi mulkin Tinubu

A rahoton da aka fitar a baya, an ji Shugabannin IMF sun nemi Najeriya ta daidaita farashin kudin waje kuma a cire tallafin fetur, kuma an yi hakan.

A cikin makonni, gwamnatin Bola Tinubu ta yi wasu cikin abubuwan da Hukumar IMF ta ke so. Hakan ya sa hukumar ta ce ta shira taimakawa kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel