Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Yayin Da Za a Ci Gaba Da Tattaunawa

Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Yayin Da Za a Ci Gaba Da Tattaunawa

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyyana cewa za su iya tsunduma cikin yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta yi musu wasa da hankali
  • Mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadagon na ƙasa, Adewale Adeyanju, shi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da ake shirin sake zama da wakilan Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana shirin tsunduma cikin yajin aiki idan ba a cimma matsaya ba a tattaunawar da ta ke da gwamnatin tarayya kan cire tallafin man fetur da ƙara mafi ƙarancin albashi.

Kamar yadda Punch ta rahoto, za a ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙungiyar ƙwadagon da gwamnatin tarayya domin samun mafita kan buƙatun da ƙungiyar ta gabatarwa da Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Jerin Muhimman Abubuwa 8 Da Gwamnatinsa Za Ta Mayar Da Hankali A Kai

Kungiyar kwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki
Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin FG da kungiyar NLC Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ƙungiyar ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata daga N30,000 zuwa N150,000 saboda cire tallafin man fetur.

A zaman da ya gabata wanda aka gudanar a tsakanin ɓangarorin biyu, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila wanda ya wakilci gwamnatin tarayya, ya bayyana cewa sun cimma mafita guda bakwai domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƙungiyar Ƙwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki idan?

Da yake magana kafin zuwan ranar zaman da sake gudanarwa a tsakanin ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin tarayya ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Adewale Adeyanju, ya ce za su tsunduma yajin aiki idan gwamnati ta kawo wargi.

Ya bayyana cewa an gabatarwa da gwamnatin tarayyar buƙatu masu yawa daga ciki har da sake farfaɗo da matatun man fetur ɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Abdulsalam Abubakar a Villa, Bayanai Sun Fito

Adeyanju, a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni ya bayyana cewa a shirye su ke su saurari abinda gwamnatin tarayyar za ta zo da shi, sannan idan bai cika abubuwan da su ke buƙata ba, za sƴ tsunduma cikin yajin aiki.

Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

A baya rahoto ya zo kan dalilan da za su sanya yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ba zai yi nasara ba.

Daga cikin dalilan akwai rarrabuwar kai da ke a cikin ƙungiyar ƙwadagon da zargin siyasantar da lamuran ƙungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng