Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

  • An dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa
  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dakatar da Bawa sannan ya umurce shi da ya mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar ta EFCC
  • Dakatarwar da aka yi wa Bawa har sai baba-ta-gani ya biyo bayan zargin da ake masa na cin mutuncin kujerarsa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), jaridar Daily Trust ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya saki a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni.

Abdulrasheed Bawa da shugaban kasa Bola Tinubu
Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewar Bassey, dakatarwar da aka yi wa Bawa ya biyo bayan manyan zarge-zarge da ake yi masa na cin mutuncin kujerarsa, rahoton TVC.

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

Bassey ya kuma bayyana cewa an yi dakatarwar ne domin bayar da damar bincike kan ayyukansa yayin da yake ofis.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya umurci Bawa da ya mika shugabanci ga daraktan ayyuka a EFCC

An umurci Bawa da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar, wanda zai jagoranci lamuran ofishin shugaban hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da dakatar da Mista AbdulRasheed Bawa, CON, daga matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) har sai baba-ta-gani domin bayar da damar bincike kan ayyukansa yayin da yake ofis.
"Hakan ya biyo bayan manyan zarge-zarge na cin mutuncin ofis da ake masa. An umurci Mista Bawa da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga darakta, ayyuka a hukumar, wanda zai jagoranci harkokin ofishin shugaban hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Kai Ni Wajen Bola Tinubu – Jonathan a Kan Ziyararsa Zuwa Aso Rock

Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewashugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kujerarsa ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel